Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Sake Saka Dokar Fita Zai Haddasa Yunwa Da Matsalolin Tattalin Arziki – MAN

by Yusuf Shuaibu
January 6, 2021
in TATTALIN ARZIKI
3 min read
MAN
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kungiyar masana’antu ta Nijeriya (MAN) reshen Abuja ta bayyana cewa, sake saka dokar hana fita da zaman gida a Nijeriya zai haifar da tsananin tsagwaron yunwa da kuma matsalolin tattalin arziki a cikin kasar bakidaya.

kungiyar ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da manema labarai a ranar Litini, inda suke mayar da martini a kan kalamun shugaban kwamitin shugaban kasa na cutar Korona, Dakta Sani Aliya, wanda a ranar Lahadi ya bayyana cewa, gwamnati ta kammala dukkan wani shirye-shirye na saka kakaba dokar hana zirga-zirga.
Aliyu ya bayyana haka ne sakamakon yawan wadanda suke harbuwa da cutar Korona suna kara yawa a cikin kasar nan, inda ya ce a mako daya an samu yawan mutane guda 6,000 wadanda suka harbu da cutar, yayin da mutum 33 cutar ta kashe su har lahira. A cewarsa, ‘yan Nijeriya ba za su taba kaucewa sake shiga cikin sabon dokar hana zirga-zirga idan suka daina saka takun-kumi da kuma wanke hannu.
Gwamnatin tarayya ta kakaba dokar takaita zirga-zirga na farko a jihohin Legas da Ogu da Babban Birnin Tarayya a ranar 27 ga watan Afirilun shekarar 2020, sakamakon barkewar cutar Korona a Nijeriya. An cire dokar takaita zirga-zirga a ciokin watan Yuli. A ranar 17 ga watan Disamba, kwamitin shugaban kasa a kan cutar Korona ta bayyana cewa, za a sake saka dokar takaita zirga-zirga sakamakon karuwar wadanda suke kamuwa da cutar Korona da kuma wadanda suke mutuwa.
A ranar 4 ga watan Disambar shekarar 2020, an tabbatar da yawan wadanda suka harbu da cutar Korona guda 68,627, yayin da adadin wadanda suka mutu suka kai 1,179. Amma a ranar Lahadi, hukumar da ke kula da cututtuka ta bayyana cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar Korona a Nijeriya sun kai 90,080, sannan wadanda suka mutu sun kai 1,311. Ko da yake, shugaban kwamitin shugaban kasa kan cutar Korona ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya za ta dauki tsauraran matakai kan lamarin ciki har da kakaba dokar takaita zirga-zirga, amma kuma mininstan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed a wajen taron manema labarai da gudana a Jihar Legas a ranar Litinin, ya ce gwamnati ta dakatar da saka dokar takaita zirga-zirga karo na biyu.
Ministan ya ce, “maganar saka dokar takaita zirga-zirga, ba na tunani akwai lokacin da gwamnatin tarayya ta ce za ta sake saka dokar takaita zirga-zirga karo na biyu. Amma dai, gwamnatin tarayya ba ta jin dadin yadda ‘yan Nijeriya ba sa bin ka’idojin kariya daga cutar Korona kamar rashin saka takun-kumi da bayar da tazara da kuma wanke hannaye, mutane suna cakuduwa waje daya.
“Idan aka ci gaba da haka, to za a ci gaba da samun karuwar masu dauke da cutar wanda za ta yi wahalar kulawa da ita, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da takurawa ‘yan Nijeriya a kan bin ka’idojin kariya daga cutar Korona.
“Gwamnatin tarayya tana sane da illar da za a iya fuskanta na tattalin arziki idan ta sake saka dokar takaita zirga-zirga karo na biyu ga ‘yan Nijeriya, domin ba zai taimaka ba wajen farfado da tattalin arziki, amma kuma rashin bin ka’idojin kariya daga cutar Korona yana da matukar mahimmanci.”
A zantawaarsa da manema labarai, shugaban kungiyar MAN, Mista Segun Ajayi-Kadir ya bayyana cewa, sake saka dokar hana zirga-zirga karo na biyu zai haddasa yunwa da matsalolin tattalin arziki ga ‘yan Nijeriya. A cewarsa, saka dokar karo na biyu zai kawo mummunar karancin rashin abinci a cikin kasar nan.
Ya ce, “ina tunanin sake bullon cutar Korona za ta haifar da mummunan yanayi. Sabodaa a dai-dai wannan lokacin ne muke bukatar zuwa wuraren aiki domin farfado da tattalin arziki, sakamakon matsin tattalin arziki da kasar nan take fuskanta a halin yanzu.”
Ya kara da cewa, kungiyar masana’antun sun tattauna a tsakaninsu wajen ganin akwai yuwuwar sake saka dokar hana zirga-zirga karo na biyu a cikin kasar nan. Ajayi-Kadir kungiyarsa za ta ci gaba da kokari wajen ganin ana bin ka’idojin kariya daga cutar Korona domin kaucewa sake shiga cikin dokar takaita ziga-zirga kawo na biyu wanda zai iya shafar ayyukan tattalin arziki a kasar nan.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

’Yan Barcelona Sun Kamu Da Cutar Korona

Next Post

Liverpool Ta Buga Wasanni Uku Ba Ta Samu Nasara Ba

RelatedPosts

Matatun

Matatun Man Nijeriya Sun Lakumi Biliyan 152.08 Ba Tare Da Tace Digon Mai Ba

by Yusuf Shuaibu
18 hours ago
0

A cikin sabon rahoton kamfanin main a kasa (NNPC) ya...

Layin Dogo

Gwamnati Za Ta Kashe Biliyan N71 Wajen Kwangilar Titinan Dogo Shida

by Yusuf Shuaibu
2 days ago
0

Gwamnatin tarayya za ta kashe kudade wajen gudanar da hanyoyin...

TAJBank

TAJBank Na Kokarin Inganta Harkokin Ilimi A Nijeriya

by Yusuf Shuaibu
2 days ago
0

Bankin TAJBank wanda yake gudanar da kasuwancinsa ta tare da...

Next Post
Liverpool

Liverpool Ta Buga Wasanni Uku Ba Ta Samu Nasara Ba

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version