An bayyana cewar sake baiwa jam’iyyar APC dama daga kasa har sama ne babbar hanyar da ta dace samu nasarar karasa muhimman aiyukan da suka faro a matakin kasa da jihar Bauchi.
Jagoran tafiyar Makama Babba Alheri 2019 kuma mamba a majalisar yakin neman zaben gwamnan jihar Bauchi, Ambasada Kkhalid Hassan ya shaida hakan a hirarsa da wakilinmu a Bauchi.
Ya ce, muddin ‘yan Nijeriya suka sake amincewa da zabar jam’iyyar APC na zaben 2019, hakan zai kawo gagarumar nasara da ci gaba, ya shaida cewar akwai fargabar Nijeriya ta sake komawa hanun wadanda suka yi wa kasar cin kaca a baya.
“Shugaban kasa ya umurci ubanmu kuma gwamnan jihar Bauchi, Muhammad A. Abubakar, ya ce yana rokon al’ummar jihar Bauchi da su yi umumu su zaba masa APC daga sama har kasa a dukkanin kujerun da suka hada da ‘yan majalisu da gwamnoni don gudun irin abun da ya faru a baya na hanjin jimina wadanda yanzu haka sun ma fita daga jam’iyyar,” in ji shi.
Khalid, ya sha alwashin cewar a jihar Bauchi shugaban kasa Buhari zai samu ninkin kuri’un da ya samu a zaben 2015, inda ya tabbatar da cewar a zaben shugaban kasa da zai gudana goben Buhari zai samu gagarumar nasara a jihar.
Arewa ya jinjina wa salon mulkin gwamnan jihar Bauchi, “a bisa tsayuwar dakatar da ya yi wajen tallata shugaban kasa a lunguna da sakona, wanda hakan zai baiwa shugaban kasa gagarumar nasara a wannan zaben. Muna fatan Allah ya sa da shi da shugaban kasa su dawo kan mulkinsu domin ci gaba da kyautata rayuwar jama’an kasa da jihar,” In ji Khalid.
“Dole ne a jinjina wa gwamnan jihar Bauchi a bisa hakurinsa da iya salun shugabanci, M.A yana kokarin kau da kansa daga irin masu suka da adawarsa, hadi da maida hankalinsa kan ci gaban jihar zalla, ko ga magoya bayansa ma, cewa yake yi duk lokacin da wani ya zage shi, kada a rama masa da zagi a bishi da bayyana manufofinsa da kyakyawawan aiyukan gwamnan, wannan ya taimaka sosai wajen rage fitinar siyasa da maida hankali kan aiyukan ci gaba,” Kamar yadda Khalid ya bayyana.
Arewa ya shaida cewar suna fatan jama’a za su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi shugaban kasa a gobe Asabar da kuma zabin gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar a zaben gwamnoni da za a gudanar a watan gobe.