Connect with us

LABARAI

Sake Zaben Buhari Alheri Ne Ga Nijeriya –Mai Dankalin Turawa

Published

on

Shugaban babbar kasuwar sayarda kayan gwari ta Afrika wadda take a Nijeriya a cikin jihar Legas Alhaji Haruna Mohammed Tamarke Mai Dankalin Turawa kasuwar Mile 12 ya bayyana cewa, ya kamata al’ummar Nijeriya su sake ba shugaban kasa Muhammadu Buhari damar komawa karagan shugabanci kasar karo na biyu domin cike kudurinsa na shigar da Nijeriya sahun kasashen duniya wadanda suka ci gaba ta fanni da ban daban a duk fadin kasar nan.

Alhaji Haruna Mohammed ya yi wannan tsokaci ne jim kadan bayan dawowarsa daga gida arewacin Nijeriya domin gudanar da bikin babbar sallar wanna shekarar, sannan kuma ya cigaba da yi wa al’mumar jihar Legas huduba da Nijeriya baki daya dasu ci gaba da ba gwamnatin Muhammadu Buhari hadin kai da goyon baya wajen aiyukanta na alheri da suke ciyar da kasar nan gaba ta hanyar kara zabarsa a shekarar 2019, shekarar zaben shugaban kasa mai zuwa domin ya kara darewa kan wannan kujera ta shugabancin kasar nan ya ci gaba kare mutuncin Nijeriya a idanuwan kasashen duniya da kuma sanya Nijeriya cikin sahun kasashen da suka ci gaba wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan da sauran ayyukan alheri da al’mumar Nijeriya zasu ci gaba da amfana a duk fadin kasar nan.

Daga nan ya ci gaba da yi wa shugaban kasar Nijeriya jagoranci da sauran gwamnonin da suke son Nijeriya ta ci gaba da fatan alheri agare su baki daya.

Alhaji Haruna Muhammed ya ci gaba da yaba wa gwamnan Jihar Katsina Hon. Aminu Bello Masari Dallatun Katsina bisa ga bin sahun shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kawo ayyukan ci gaba da za su taimaki jama’ar jhar Katsina da Nijeriya baki daya sannan ya umurci al’ummar jihar Katsina dasu ci gaba da goya wa Gwamnatin Hon. Aminu Bello Masari baya domin ya ci gaba da kawo aiyyukan raya kasa a fadin jihar, sannan ya ci gaba da yaba wa Gwamnan Jihar Legas Akinwunmi Ambode a kokarinsa a hada kan al’mumar Yarabawa da sauran kabilu mazauna Jihar Legas da kuma kawo ayyukan raya kasa ga al’mumar Jihar Legas za su ci gaba da amfana sannan ya nuna farin cikinsa da godiya ga shuwagabannin kasuwar Mile 12 na bangare daban daban wajen bashi hadin kai da goyon baya a wajen al’amuran da suka shafi kasuwar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: