Wasu manoma Jihar Sakkwato sun bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta iya samar da kusan Naira biliyan 150 a cikin shekaru hudu daga noman dabino.
Muhammed Maidoki, shugaban kungiyar masu noman dabino, sarrafawa da kuma sayar da shi reshen jihar Sokoto (ADAFPAM) me ya bayyana hakan a hirarasa da maenma labarai a jihar a ya yin duba wata katafariyar gonar dabino a jihar da za ta Iya samar da tan 100,000 nan da shekarar 2024.
A cewar shugaban kungiyar masu noman dabino, sarrafawa da kuma sayar da shi reshen jihar Sokoto, aikin zai samar da ayyuka kai tsaye guda 72,000, tallafawa ayyukan kai tsaye 840,000 da samarwa gwamnatin jihar kudaden shiga sama da Naira biliyan 150 a duk shekara.
Muhammed Maidoki, shugaban kungiyar masu noman dabino, sarrafawa da kuma sayar da shi reshen jihar Sokoto ya ce, hasashen ya kai kimanin kashi 10 cikin 100 na noman dabinon na Masar, wanda shi ne na farko a duniya wajen samarwa, inda ya ci gaba da cewa, tun daga nan gwamnatin jihar ta kafa shuka ta dabino ta biyu mafi girma a kasar.
A cewar shugaban kungiyar masu noman dabino, sarrafawa da kuma sayar da shi reshen jihar Sokoto, mun kafa wani shiri na sa kai na matasa a duk makarantun sakandaren dake jihar don kafa akalla kadada daya ta gonar dabino a kowace makaranta., inda ya kara da cewa, wannan yana aiki a halin yanzu a cikin makarantu 20 kuma da sannu zai isa har zuwa makarantu 500 a cikin jihar.
Shugaban kungiyar masu noman dabino, sarrafawa da kuma sayar da shi reshen jihar Sokoto, ya ce, wannan hanyar za ta shirya tsara wacce za ta samar da kayan aiki don gudanar da dukkan lamuran hada-hadar noman dabino, kuma da fatan za a sanya jihar a matsayin babbar cibiya a harkar noman dabino da kuma sarrafawa, inda shugaban ya kara da cewa, gwamnati ta sayo ingantattun itacen dabino 40,000 daga Cibiyar Nazarin Dabino ta Nijeriya kuma an rarraba wa mutane da al’ummomin jihar.
Shi ma, shugaban kungiyar ADAFPAM na kasa, Dakta Hassan Dikko, ya ce an kafa kungiyar ne da nufin bunkasa noman, sarrafawa da kuma sayar da dabinon a Nijeriya, inda ya kara da cewa, tun da dadewa ba a kula da gonakin dabinon, kuma suna da matukar karfi na ganin kasar ta ci gaba ta fuskar tattalin arziki.
Shugaban kungiyar Dakta Hassan Dikko, ya ce, kafin yanzu, kasashe da yawa sun dogara da samar da dabino a matsayin babbar hanyar samun kudaden shiga, inda ya kara da cewa, wadannan kasashe sun sami ci gaba ne bisa la’akari da kudaden shiga da ake samu daga itacen dabino.
A cewar shugaban kungiyar Dakta Hassan Dikko, a gare mu mu bunkasa tattalin arzikin kasar nan, muna ganin yana da muhimmanci mu kafa wannan kungiyar.