A ‘yan kwanakin nan wakar ‘Mai Hakuri’ ta fitaccen MAWAKI SADEEK ZAZZABI, ta bayyana a gari, wacce kuma ta zamo wakar da aka fi sauraron ta a dan tsakanin nan, musamman ma dai a dandalin sada zumunta. Duk da cewar, ba ita ce wakar Sadeek Zazzabi da ta yi fice da kuma daga darajarsa ta farko ba, amma za a iya cewa, ita ma wakar Mai Hakuri ta kara darajar mawakin, saboda irin salonta da kuma abubuwan da ta kunsa. Ganin irin karuwar da wakar ta yi da kuma sakon da ya ke cikinta ne ya sa LEADERSHIP A YAU ta nemi jin ta bakin Sadeek Zazzabi, domin ya bayyana wa masu karatunmu irin salon salon wakar da kuma sakon da yake cikinta. Ga yadda hirar ta kasance:
Shin me wakar Mai Hakuri ta kunsa?
Ita wakar Mai Hakuri waka ce da na yi ta a kan karfafa gwiwa don haka na yi wakar ne don na nuna cewar tabbas Mai Hakuri ya kan cimma rabo, kuma duk wani mataki da ka ga mutum ya kai kuma ya yi nasara a rayuwa, sai da ya yi Gwagwarmaya a yi kamar ba a yi ba kafin a kai ga nasara. Saboda haka sai na saka wa wakar suna Mai Hakuri zai tadda rabo don na karfafa wa masu neman nasara a rayuwa gwiwa a kan su yi hakuri, kuma hakurin ba Wai na ka bar abin ba a a ka yi hakuri da juriya a kan neman abin da ka sa a gaba wajen neman sa don ka cimma nasara.
Wakar ta zo da wani sabon Salo daban wanda kowa zai fahimci sakon da ya ke cikin ta ba kamar yadda sauran wakokin suke ba?
Eh, to ai bai kamata abin da ka ke yi wajen isar da sako musamman ma waka ka boye wasu kalmomi ba, domin idan ka yi haka to Gudummawar da za a bayar ba ta fito ba tun da so na ke na fadakar ya kamata na yi abin da za a fahimce shi, wannan ya sa na fito da sakon a bayyane, don ba kamar irin wakar siyasa ba ce wacce za a yi kamar Dinka riga ba wuya, to wannan kuma ya kamata a yi ta a bayyane don ya zama an fitar da sakon ya tafi don ya amfanar da Jama’a.
Ita wannan wakar an ji ta ba ta da tsayi ko tsawon ta zai kai minti nawa?
Haka ne ka san yadda wakar isar da sako ta ke, abin da a ke bukata sakon ya Isa ba sai an yi baituka masu yawa ba, don ita wakar Mai Hakuri, baitukan ta biyar ne kuma tsawon minti uku ce, amma ka ga yadda sakon ya Isa a yanzu kowa sai maganar wakr ya ke yi.
A cikin wakar akwai wani baiti da ka ke cewa “Shi ko rago ba ya nasara, ko a gida bai samun ta, me ke ke nufi a nan?
To ai tun farkon baitin za ka ji ina cewa” Ka san dukkan nin nasara da ta ta ta aka fara ta, domin dukkan nin nasara da mai ita ne aka fafata. Ko ba dade ko ba jima ai Mowa aka fifita. Ni kuma mai neman Lada, ai Allah na ka yi wa bauta. Shi kuwa rago ba ya nasara ko a gida bai samun ta “. Abin da na ke nufi a nan ita nasara ko a cikin gidan ka ne, idan ba ka nemeta ba to ba za ka samu ba. Kuma duk ina kawo wannan misalin ne don me nema ya zabura ya ci gaba da neman ta.
To, wato ita wannan wakar zango na farko ne, sai nan gaba za a ji na biyun?
A gaskiya ka san duk wani abu da ka dauka ka yi waka za ka same shi yana da dan zurfin, sai dai ka dauki abin da ka ke ganin za ka dauka ko Yaya sakon ya je don haka a yanzu dai ba ni da tunanin a kwai Zango na biyu sai dai idan yanayi ya bayar za a ga cewar akwai damar za a je Zango na biyun, amma dai a yanzu ba ni da wannan tunanin, sai dai na dakko wata matsalar in gina waka a kan ta. Kamar dai yadda a baya na yi waka a kan Wadatar Zuci, na yi waka a kan Matsalar aure, na yi waka a kan matsalar Nigeria matsalar shugabanni da mu mabiya, wadda na yi wa taken Mu dau aniya ta gyara. Bayan wannan na yi waka a kan matsalar Fyade. To yanzu ma ina kan wani yunkuri wanda na ke tunanin nan da dan wani lokaci idan na yi wata wakar za ta bayar da gudummawa ga Jama’a kan gyara da kuma karfafa gwiwa.
Ko wanne irin buri ka ke da shi nan gaba a bangaren waka?
To, burina dai shi ne baiwar da Allah ya ba ni ya zama na tafiyar da ita ta hanyar da ta dace, don ya zama ko da ba na raye ‘ya’ ya da jikoki sun yi alfahari da abin da na muka yi domin ba ni da wani buri da ya wuce cewar basirar da Allah ya ba ni, ya zama na yi amfani da ita ta hanyar da ta dace, wannan shi ne babban burina. A kan samu wasu daga cikin fitattun mawaka da ‘yan fim da su ke kafa Gidauniyar tallafa wa jama’a, wada ko bayan ba sa nan ana tunawa da su, ko kai ma kana da irin wannan a nan gaba?
To, ita maganar Gidauniya domin tallafa wa jama’a tun tuni na samar da ita, don ba zan manta ba tun a shekarun baya da na yi wata waka ta siyasa wadda a sanadiyyar ta ne na yi zaman gidan yari, kuma na ga halin da su ke ciki wanda sai ka ga wani a kan dan karamin bashi an kai shi ya shafe wata da watanni ya sa na samar da Gidauniya bayan na fito, wanda na ke zuwa ina kubutar da irin wadannan mutanen masu kananan basuka da kuma wadanda wani tsautsayi ya kai su kuma suna bukatar a fitar da su, to wannan aikin Gidauniya ta ta saka a gaba kuma Alhamdulillah har yanzu muna ci gaba da yin wannan aikin. Sai dai ni tawa Gidauniya ba ina neman tallafi ba ne daga wajen wasu kamar yadda sauran su ke yi, ni ina yi ne da dan abin da Allah ya hore mini, don haka sai na yi wani tsari a shekara abin da na samu sai na fitar da wani kaso don gudanar da aikin Gidauniyar, saboda haka ba wasu kudade na ke samu daga wani waje ba Wana ne na ke fitar wa daga aljihuna domin bayar da tawa gudunmawar, kuma Ina fatan abin ya dore har karshen rayuwata.
Mene ne sakonka na karshe?
To sako na dai na karshe ga masoya na ne Ina Kara godiya a gare su kuma ina alfahari da su, kuma ga duk wanda ya ke bukatar wakoki na sai ya neme ni a shafina na You Tube ko Instagram da sauran shafukana domin sauraron wakokina na bidiyo da na Oudio, ina fatan alheri ga kowa da kowa nagode sosai Allah ya bar zumunci.