Ammar Muhammad" />

Sakon Fatan Alhairi Daga Kungiyar Raya Kasa Ta RAYAAS

Muhimmiyar Sanarwa Daga Kwamitin Shirya Taron Kasa Na Bauchi

Assalamu Alaikum warahmatullahi, Edita barka da aiki.

Ina yi wa duk kanin al’ummar Rayaas fatan alkairi adai dai wannan lokaci, sako na musamman ga dukkanin mai kishin cigaban RAYAAS. Wannan kwamiti mai albarka bisa zama da ya yi na musamman agarin Gombe, satin da ya gabata ranar Lahadi 7-10-2019, ‘yan kwamitin sun yunkuro gaya don ganin an samu nasarar yin wannan taro cikin nasara.

Kan haka ta kuduri aniyar fara raba takardun neman izinin ganawa da dukkanin wanda aka san mai taimakawa ne kan sha’anin kungiyoyi, walau Patron na kungiya, dan Siyasa, dan kasuwa, NGO’s, basarake ko wani Shugaba.

Nan take ‘yan kwamitin sun samar da sunayen mutane akalla 20, Kuma tana cigaba da karbar sunayen don tura musu da neman takardar ganawa.

Abin da buke bukata shi ne: 1- Sunan wanda zai taimaka. 2-Wanda zai isar mana da takardarmu gareshi. 3- Amincewar shi da kuma samun lokacin ziyarar. Kwamitin namu zai kai ziyarar ne tare da wanda ya nemo mana izini, Shugaban jiha, Nat Secretary da kuma Coodinators dinmu.

Kada ku manta kwamitin namu tun farko yana aiki ne kafada da kafada tareda Nat Org Secretary da izinin Mai girma Nat Chairman. Kwamitin Sun shirya tsaf don zagaye kasarmu, matukar kannan kungiya za ta yi nasara kan wannan babban taro namu. Yana da kyau ku tuna cewa Taronmu yamatso, yau Sauran Sati 6 kawai. Kuma Insha Allahu zamuyi wannan aikin ne cikin wannan watan (10). Don Allah muna bukatar Sunayen da wuri.

Kwamitin Suna mika sakon godiyarsu ga dukkanin wadanda suka bada tasu gudummawar.

Allah ya kara daukaka mana wannan kungiya ta mu mai Albarka ya kuma bamu ikon yin wannan taro cikin nasara Amin. Sako daga Shugaban Kwamitin shirya taron kasa na Bauchi 2019, AFFAN IBRAHIM,  Amadadin Sauran ‘yan Kwamiti.

Rayuwarmu Ayau Youth Awareness Association Rayaas Gombe state Chapter

Mai gabatar da kasida ta gaba shi ne Dakta Adamu Umar lakcara Jami’at Gombe (GSU) Dakta ya bayanai masu kama hankali tare da Jan hankalinki matasa bisa yanda muka dauki soshiyal midiya ta zama kafa Ko fage na cin karenmu Ba babaka Don kuwa Wanan kafa bata da mafadi bare Mai ladabtarwa yaja hankalin matasa dasu dage da yada manufofi nagari kamar irin Wanan kungiya da ta gaya to shi Wana Taro tareda yiwa Wanan kungiya fatan alkhairi da nasara da cigaban Wannan kungiya. Jabeer M. Haruna National media team, Gombe State Director Media 08163048588

Sakon Ta’aziyya

A Madadin Shugabanan Wannan Kungiyar Mai Albarka Wato (Rayaas) Reshan Jihar F.C.T. Abuja da kuma Arewa ta Tsakiya (North Central) da daukacin manbobinta baki daya mukemika sakon ta’aziyyar mu ga iyalan gidan Dakta Adam Dangambo Suleja.

Da ‘yan uwa baki daya bisa rashin dan uwanmu Alhaji Jibrin Dan’asabe. Muna rokon Ubangiji Allah ya gafarta masa. Allah ya jikansa da rahama! ameen. Sako daga Surajo Bala Salihu. (Zonal Youth Leader). Amadadin Chairman North Central, Alhaji Nasiru Isa Garun Malam.

Rahoton Bayan Taron Kungiyar RAYAAS Shiyyar Arewa Maso Gabas.

Salam Edita muna yi maka fatan alheri

Bayan bude taro da sunan Allah mai rahama mai jinkai tare rokon Allah madaukakin sarki ya sanya mana albarka cikin abin da za mu tattauna a lokacin, nan ta ke aka fara gabatar da manyan baki na musamman, daga nan sai jawabin maraba daga bakin shugaban kungiya reshen Jihar Gombe da jama’arsa.

Bayan wannan kai tsaye muka wuce zuwa ga sauraron takaitaccen tarihin kungiya tun farkon kafuwarta zuwa yau, da irin gwagwarmayar da aka sha, nasarorin da ta samu cikin shekaru biyu da kuma kalubalen da take fuskanta, daga bakin Dan Masanin RAYAAS, da kuma sauran jawabai daga manyan bakin da su ke saman tebur, wanda su ka hada da, Shugabannin Kungiya na Kasa, da kuma shugabannin shiyya, inda su ka bayyana mana makasudin shirya wannan taro da kuma abubuwa guda biyar (5) da wannan yanki namu zai fi mayar da hankali cikin shekarar 2020 da zamu shiga da izinin Allah.

Wanda mai girma shugaban kungiya na yankin Arewa maso gabas, Malam Usman B. Adams ya ba da umarni a karanto ajandojin daya bayan daya, kowa ya ji, sannan a bai wa jama’a dama su tofa albarkacin bakunan su a wajen. Bayan haka mutum zai iya ba da shawararsa a rubuce ta hannun sakatare ko shugaban kungiya reshen jiharsa.

Ga dai Abubuwa da muka tattauna Guda biyar kamar haka:

1. Yadda za mu dauki nauyin shirya babban taron kungiya ta kasa baki daya da muke shirin gudanarwa a Jihar Bauchi, a farkon watan sha biyu da izinin Allah.

2. Tsare-tsaren kama ofishin kungiya na shiyyar Arewa maso gabas a Jihar Gombe, tare da zabar wakilan da za su duba wurin da ya kamata mu kama cikin wannan shekara.

3. Hanyoyin da zamu bi wajen samarwa shiyyarmu da jihohinmu na Arewa maso Gabas kudin shiga ba tare da an dorawa mambobin kungiya nauyi ba.

4. Fadada ayyukan taimakon juna tare da yunkurin kafa wata gidauniya domin taimakawa mambobin kungiya musamman ‘yan Arewa maso Gabas.

Misali: Idan wani ibtila’i ya samu dan kungiya na asarar dukiya ko rashin lafiya kungiya za ta dauki nauyin dawainiyar jinyarsa da iyalinsa, har zuwa lokacin da Allah zai ba shi lafiya. Sannan wanda ya rasu wannan gidauniya da za mu kafa in sha Allahu za ta dauki nauyin karatun ‘ya ‘yansa akalla zuwa lokacin da za su gama sakandire, ko jami’a.

Haka nan duk dan kungiya da yabar ‘ya ‘ya mata marayu kungiya ce za ta dauki nauyin aurar da su, ga mijin da su ka zaba da kansu, tare da duk wata dawainiyar bikin aure.

5. Kaddamar da fara shirin koyawa mata da matasa kananan sana’o’in hannun tare da ba su jarin farawa da kuma takardar shaidar kammala abin da su ka koya, inda aka nada kwamiti na musamman karkashin jagorancin, Alhaji Umar Shuaibu Abukar (U.S.A BABAWO chairman

B. Hajiya Maryam Aliyu Kobi (Mai Sarauta) Sakatariya  C. Ali Wakil Jajimaji  (Member) D. Aminu Mohammed Borno (Member) E. Malam Babayo Sale (Member) da sauran wasu muhimman batutuwa da su ka shafi ci gaban kungiya a matakin kasa baki daya. Da fatan Allah madaukakin sarki ya taya mu riko kuma ya jagorance mu, amin.  Na gode, Na ku Auwali Differences Sakataren Tsare-Tsare Na Kasa Baki Daya.

Muna Tunatar Da Daukacin Mambobi Da Shugabannin Kungiya Game Da Gudummuwar Kudin Taron Kasa

Account Name: Rayuwarmu Ayau Youth Awareness Association Account number: 5960318018 Bank Name: FCMB Contact number: 08026268848, 08065992369

Ka da a manata National Edco N3000, Zonal Leaders N2000, Shugabannin Jihohi N1500

Mataimakansu  N1000 Sakatarorin Jihohi N500, Masu rike da Sarauta N1000

Mamba Ya Ba da Abin da Ya sauwaka Gare Shi

Kowa zai iya ninka gudummuwar kudin da zai bayar fiye da abinda aka fada, saboda ci gaban kungiya. Bayan haka idan akwai wanda zai dauki nauyin komai gameda taron muna maraba da shi, kofa a bude ta ke.

Exit mobile version