Abba Ibrahim Wada" />

Salah Ya Ji Ciwo A Wasan Misra

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Muhammad Salah, yaji ciwo a kafarsa a wasan daya wakilci kasarsa ta Masar a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za’a buga a kasar Kamaru a shekara mai zuwa.

Salah dai yaji ciwon ne bayan daya buga wata kwallo ta kusurwa duk da cewa ya ci kwallon amma kuma dole yafita daga wasan bayan da likitoci suka tabbatar da cewa bazai iya wasan ba.

Kasar Masar dai ta buga wasa ne da kasar Swaziland a birnin Cairo a wasan da suka samu nasara da ci 4-1 kuma Salah din ya zura kwallo a raga a farkon wasan.

Tun farko dai an tsara cewa ‘yan wasan kasar Masar zasu buga wasa na biyu da kasar ta Swaziland a can kasar ta Swaziland din amma kamar yadda rahotanni suka bayyana dan wasan mai shekara 26 bazai buga wasan ba a ranar Talata.

“Bayan wasan Salah ya gayamana cewa yanada matsala a kafarsa kuma mun duba likitoci sun tabbatar da haka saboda haka mun yanke hukuncin cewa bazai bimu wasa na biyu ba zai koma kungiyarsa ne domin ya ci gaba da samun sauki” in ji kociyan kasar ta Masar

Liverpool dai za ta dawo buga wasan firimiya ne a sati mai zuwa lokacin da za ta kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta Huddersfield a ranar 20 ga wannan watan da muke ciki.

Exit mobile version