Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp, ya tabbatar da cewar dan wasan gaba na kungiyar Muhammads Salah ya warke daga cutar Korona kuma ya fara daukar horo a jiya Litinin.
Tun farko daman dan wasan tawagar kasar Masar din ya bayyana cewa babu wata damuwa a tattare dashi kuma nan gaba kadan zai warke daga cutar Korona wadda ta kamashi a satin daya ganata lokacin da yaje wakiltar kasarsa ta Masar a wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Africa.
Gwaji ne ya tabbatar da cewa Salah yana dauke da cutar ta korona yayin da ya tafi bugawa kasarsa ta Masar wasa kuma hukumar kwallon Masar ce ta tabbatar a satin daya gabata cewa Salah mai shekara 28 a duniya, sakamakon gwajin Korona da a ka yi ma sa ya nuna yana dauke da cutar.
Da ma dai Salah zai killace kansa kuma ya kaurace wa buga wa Liverpool wasan ranar Asabar da Liverpool ta karbi bakuncin Leicester City a Premier League a wasna da suka samu nasara daci 3-0 sai dai zai iya buga wasa da kungiyar Atalanta a filin wasa na Anfield a gasar zakarun Turai.