Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana cewa kawo yanzu dan wasan gaban kungiyar, Mo Salah, ya zama babban jagoran kungiyar biyo bayan zura kwallayen da yake yi a halin yanzu.
Mohamed Salah ya ci kwallo a karon farko bayan wasanni 7 a wasan gasar Firmiyar Ingila, inda ya antaya wa kungiyar kwallon kafa ta West Ham kwallaye biyu a raga, abin da ya taimaka wa Liverpool haurawa zuwa matsayi na uku a teburin gasar.
Bayan da Liverpool din suka gaza yin katabus a zubin farko na wasan, ana dawowa hutun rabin lokaci ne suka ga dacewar shafa wa kansu lafiya, inda , sakamakon haka ne Salah saka kwallon farko a raga.
Bayan mintina 11 da cin kwallon farko ne Salah ya kara ta biyu, bayan da dherdan Shakiri ya kawo mai wata kwallo, shi kuma bai yi wata wata ba ya dirka ta a raga, mai tsaron gidan West Ham, Lukasz Fabianski ya gaza kamawa.
Sadio Mane da Roberto Firmino ba su fara wannan wasa ba sakamakon raunin da su ke jinya, amma duk da haka Salah bai yi kasa a gwiwa ba wajen cire wa Liverpool kitse a wuta, ya kuma kawo karshen kamfar cin kwallaye.
dan wasan Brazil wanda shima a ‘yan kwanakin nan baya zura kwallaye, Roberto Firmino, ya shigo wasan daga baya, ya kuma saka wa Georginio Wijnaldum kwallon da ta kai shi ga cin kwallon Liverpool ta uku a wasan