Connect with us

WASANNI

Salah Ya Zubar Da Fanareti Biyu A Wasan Misra Da Nijar

Published

on

A wani wasa mai ban mamaki da aka buga a kasar Masar (Egypt), Muhammad Salah wanda ya zura kwallaye 43 a Liberpool a kakar wasan data gabata ya zubar da Fanareti har guda biyu a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa.
Tun da farko dai anyi zaton dan wasan wanda yake takarar zama gwarzon dan kwallon da Modric da Ronaldo bazai buga wasan na Egypt ba amma daga baya kuma hukumar kwallon kafar kasar ta tabbatar da cewa zai buga wasan.
Salah da hukumar kwallon kasar dai sun samu rashin jituwa ne kwanakin baya sakamakon bada dama da sukeyi kamfanoni suna amfani da hotunansa domin talla batare da saninsa ba ko kuma suna karbar kudi bai sani ba.
‘Yan wasa Marwan Mohsen da Ayman Ashraf ne dai suka fara ciwa kasar Masar kwallaye biyu sai daga baya kuma Salah yasamu bugun fanareti ya buga mai tsaron ragar kasar Niger Kassaly Douda ya ture.
Sai dai daga baya Salah yasake samun wani bugun ya sake bugawa mai tsaron ragar ya sake turewa sai dai daga baya yabi kwallon ya sake bugawa ta shiga raga sannan daga baya kuma ya sake samun dama ya zura kwallonsa ta biyu a raga.
Dan wasan Arsenal, Muhammad Elneny, shima ya zura kwallo a raga kuma wanann ne karo na farko da kasar Masar ta samu nasara a wasa tun kafin fara gasar cin kofin duniya kuma wannan ne karo na farko da sabon kociyan kasar, Jabier Maguirre ya buga wasa tun bayan fara aikin kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: