Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Salah Yana Son Barin Liverpool

by Abba Ibrahim Wada
December 23, 2020
in WASANNI
2 min read
Salah
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohammed Salah ya bayyana yiwuwar raba gari da tawagar ta sa nan gaba kadan, dai dai lokacin da kungiyar ke komawa matsayin jagorar shirin lashe gasar Firimiya karo na biyu a jere.

Yayin wata zantawar abokin wasan Salah dan Masar a tawagar kasa da jaridar wasanni ta AS Mohamed Aboutrika ya ce ita kanta Liverpool na kokarin sayar da dan wasan mafi zura mata kwallo a raga a halin yanzu, ko da ya ke tuni kocin Liverpool din Jurgen Klopp ya musanta batun.
Aboutrika ya ce Muhammad Salah mai shekaru 28 a duniya ya fusata matuka da yadda kungiyar ta ki bashi mukamin Kyaftin yayin wasansu da kungiyar Midtjylland karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai na Champions League maimakon haka sai ta bai wa abokin wasansa Trent Aledandre Arnold jagorancin saboda rashin Jordan Henderson.
Sai dai Mohamed Aboutrika ya ce ko kadan halin bacin ran da Salah ke ciki a Liverpool ba zai sauya salon buga wasansa ba hasalima shi ne ya zura kwallo guda da ta basu nasara a wasan nasu da Midjtyllan wanda aka tashi kwallo 1 da 1, ya yinda a karawar Asabar din nan ma ya zura kwallaye 2 duk da cewa ba a faro wasan da shi ba.
Matukar dai ta tabbata Salah zai raba gari da Liverpool zai zama babban gibi ga kungiyar wanda ke kokarin sake dage kofin Firimiya a karo na  biyu duk da cewa akwai kungiyoyi da dama da suke bibiyar bayan Liverpool kamar Tottenham da Chelsea da kuma Manchester United.
Zuwa yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce ke kan gaba a jerin kungiyoyin da suka jima suna farautar dan wasan, kuma dama shi kansa dan wasan masoyin Real Madrid ne tun yana karamin yaro.
Amma kuma banda Real Madrid kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana ganin Salah ne zai iya maye mata gurbin Leonel Messi a kungiyar idan har Messi yabar kungiyar a kakar wasa mai zuwa kuma shugabannin na Barcelona sun fara tunanin yin Magana da wakikin dan wasa Salah da kungiyar Liverpool akan ko zasu sayar musu da dan wasan wanda ya koma Liverpool daga kungiyar Roma.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Dan Wasan AC Milan Rafael Ya Kafa Tarihin Zura kwallo Mafi Sauri

Next Post

EFCC Ta Cafke Wadanda Ake Zargi Da Zambar Intanet 32

RelatedPosts

Chelsea Ta Sallami Kociyanta, Frank Lampard

Chelsea Ta Sallami Kociyanta, Frank Lampard

by Abba Ibrahim Wada
8 hours ago
0

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta sallami mai horar da...

Aguero

Barcelona Za Ta Dauki Aguero A Kyauta

by Abba Ibrahim Wada
18 hours ago
0

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta shirya tattaunawa da dan...

Tsaron Raga

Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Mai Tsaron Ragar Super Eagles

by Abba Ibrahim Wada
20 hours ago
0

Shugaban kasa Mohammadu Buhari ya aike da sakon ta'ziyarsa dangane...

Next Post
EFCC

EFCC Ta Cafke Wadanda Ake Zargi Da Zambar Intanet 32

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version