Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Muhammad Salah, zai iya barin kungiyar da zarar an kammala kakar wasa ta bana sakamakon rashin jin dadin zaman kungiyar a halin yanzu.
A satin daya gabata ne wasu rahotanni suka bayyana cewa Salah ya fara shirin hada kayansa domin barin kungiyar inda kuma tuni aka fara danganta dan wasan da komawa daya daga cikin kungiyoyin da suke bibiyarsa, wato Real Madrid da Barcelona.
Sai dai a hirar da yayi da manema labarai a ranar Juma’a, kociyan kungiyar ta Liverpool Jurgen Klopp, ya bayyana cewa kungiyar ba zata sayar da Salah ba duk da rade radin da ake cewa Salah yana son barin kasar Ingila a karshen kakar wasa ta bana.
A karshen satin daya gabata ne dan wasan gaban na Liverpool, ya bayyana yiwuwar raba gari da tawagar ta sa nan gaba kadan, dai dai lokacin da kungiyar ke komawa matsayin jagorar shirin lashe gasar Firimiya karo na biyu a jere.
Aboutrika ya ce Muhammad Salah mai shekaru 28 a duniya ya fusata matuka da yadda kungiyar ta ki bashi mukamin Kyaftin yayin wasansu da kungiyar Midtjylland karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai na Champions League maimakon haka sai ta bai wa abokin wasansa Trent Alexandre Arnold jagorancin saboda rashin Jordan Henderson.
Sai dai Mohamed Aboutrika ya ce ko kadan halin vacin ran da Salah ke ciki a Liverpool ba zai sauya salon buga wasansa ba hasalima shi ne ya zura kwallo guda da ta basu nasara a wasan nasu da Midjtyllan wanda aka tashi kwallo 1 da 1, ya yinda a karawar Asabar din nan ma ya zura kwallaye 2 duk da cewa ba a faro wasan da shi ba.
Matukar dai ta tabbata Salah zai raba gari da Liverpool zai zama babban givi ga kungiyar wanda ke kokarin sake dage kofin Firimiya a karo na biyu duk da cewa akwai kungiyoyi da dama da suke bibiyar bayan Liverpool kamar Tottenham da Chelsea da kuma Manchester United.
Zuwa yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce ke kan gaba a jerin kungiyoyin da suka jima suna farautar dan wasan, kuma dama shi kansa dan wasan masoyin Real Madrid ne tun yana karamin yaro.
Amma kuma banda Real Madrid kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana ganin Salah ne zai iya maye mata gurbin Leonel Messi a kungiyar idan har Messi yabar kungiyar a kakar wasa mai zuwa kuma shugabannin na Barcelona sun fara tunanin yin Magana da wakikin dan wasa Salah da kungiyar Liverpool akan ko zasu sayar musu da dan wasan wanda ya koma Liverpool daga kungiyar Roma.