Connect with us

DAGA NA GABA

Salihu Jankidi: Gwarzonmu Na Mako

Published

on

Malamin waka sarkin Taushin Sarkin Musulmi Abubukar na 111 Salihu Jankidi kenan.
Salihu Jankidi mutumin Rawayya ne wanda a halin yanzu take karkashin hukumar Kwatarkwashi. An haifi Jankidi a garin Rawayau a shekara ta 1852. Sunan mahaifinsa Alhassan kakansa kuwa shi ne Giye da ake yi wa lakabi da Dantigari mai abin kida mahaifiyarsa kuwa it ace Hadijatu wadda ake yi wa lakabi Umma tsohhuwa. Ya sami lakabin jankidi ne an ce a lokacin da kanen mahaifiyarsa ne ya je karbar jinjirin sai ya lura da jan da Allah ya yi masa sai ya ce Barakallah wanga da umma jan kidi. Tun daga wannan lokaci wannan lakabi ya bi shi.
Mahaifin Jankidi makadin kalangu ne kuma shi mutum ne mai sha’awar yawace-yawace kida ya ziyarci kasashe da garuruwa da yawa domin kida. Garuruwan sun hada da Argungun da Birnin Kabi da Bidda da Kwantagora da sauransu. Mahaifin Jankidi ya yi wa sarkin Sudan Ibrahim wakoki mafi yawa daga cikin wakokinsa ya yi masa su ne a fagen yaki.
Duk da an haifi Jankidi a Rawayya amma bai budi ido a nan ba sai a Kwantagora. Jankidi mutum ne mai hazaka kuma ya san dabarun fada da kare kai musamman a lokacin babu kwanciyar hankali sosai. Ya yi dambe da kokawa. Jankidi ya yi rayuwarsa ta kuruciya ne kafin mulkin mallaka don haka duk kuruciyarsa na mazakuta ne.
Salihu Jankidi ya yi karatun alkur’ani har ya sauke ya kuma karanta wasu daga cikin kananan littattafai kamar kawa’idi da ishmawi da kurdibi da iziyya da sauransu.Sai dai bai ci gaba da wani karatu ba saboda harkar kidi ta dauke masa hankali. Jankidi ya gaji waka gaba da baya yawancin zuriyarsu makada ne da mawaka don haka za a iya cewa Salihu tun da ya yi wayo ya tashi ya ga kalangu a wuyansa.
Salihu Jankidi ya karbi kida a hannun mahaifinsa daga lokacin da aka koya masa Kuntukuru. Jankidi ya koyi kidan kalangu a wajen makada Danyawuri har ya kware a wajensa sosai. Bayan rasuwar mahaifinsa ya dauki kidan kalangu ya ci gaba da gabatarwa a garin Kwantagora
A dalilin yake-yake da Turawa suka yi har ta kai an fasa garin Kwantagora Salihu jankidi shi ma ya tashi da iyalansa ya koma kasar Anka daga nan ya koma Bungudu sai ya sake komawa Kwantagora da ya lura kurar yakin ta lafa.Bayan wani lokaci kuma sai ya koma sai ya koma gida Rawayya
A tsakanin shekara ta 1903 zua 1915 lokacin yaki ya kare da Turawan mulkin mallaka sai Salihu Jankidi ya koma garin Tsafe har zuwa mulkin ‘Yantodo Abdullahi (1928-1948)Daga nan sai ya tashi daga tsafe ya koma Gusau lokacin mulkin sarkin Katsinan Gusau Muhammadu mai akwai. Jankidi ya ji dadin zaman garin Gusau inda ya mallaki gida babba da zuriyarsa ta kara fadada. Akwai inda yake nuna hakan a wakarsa inda yake cewa:-

Jagora :Ni Jankidi ba ni zuwa ko’ina’
‘Y/Amshi: Kwadaina ba shi wucewa Gusau.
Bayan da aka fitar da sarkin Katsinan Gusau Muhammadu mai’akwai aka nada shehu dan Sama’ila (1943-1945) sai salihu Jankidi ya koma wajen sarkin musulmi Abubakar 111 ya zama shi ne ubangidansa. An nada sarkin Salihu Jankidi sarkin taushin sarkin musulmi. An yi gagarumin biki a lokacin da aka nada Jankidi wannan sarauta an yi shagulgula daban-daban don taya shi murna a kan samun wannan sarauta babba ta kida.Sarkin musulmi Abubakar na 111ya nada wa Salihu sarauta a gidansa da ke Gusau.
Sarkin taushi Salihu Jankidi ya kamu da rashin lafiya ta dan karamin lokaci wadda ta zama ita ce ajalinsa. Ya rasu yana da shekara 120 a duniya ya rasu ranar 13 ga watan oktoba 1973. Allah ya jikansa da gafara amin.
Mun sami wannan tarihi ne a cikin littafin Sarkin Taushi Salihu Jankidi wanda Sa’idu Muhamadu Gusau ya wallafa.
Advertisement

labarai