Daga Abba Ibrahim Wada,
Alkaliyar wasa Salima Mukansanga ta kafa tarihin macen farko da ta fara busa a gasar cin kofin nahiyar Afirka a karawar da Zimbabwe ta ci Guinea 2-1 a fafatawar karshe a rukuni na biyu ranar Talata.
A wasan, tawagar ‘yan wasan Guinea ta kai zagaye na biyu duk da rashin nasarar da ta yi a hannun Zimbabwe, wadda ta yi ban kwana da gasar bana da ake yi a Kamaru duk da cewa Zimbabwe ce ta fara cin kwallo biyu ta hannun Knowledge Musona da kuma Kudakwashe Mahachi.
Kyaftin din Guinea, Naby Keita ne ya zare daya a wasan da suka yi a Yaounde da alkaliya, Salima Mukansanga ta kafa tarihi a babbar gasar ta Afirka.
Salima, ‘yar kasar Rwanda, mai shekara 35 ta zama macen farko da ta yi busa a gasar kofin Afirka tun da aka kirkiri wasannin.
Sannan Guinea ce ta yi ta biyu a rukuni na biyun a kan Malawi ta uku, wadda ta tashi wasa da Senegal ba ci.