Salima Mukansanga: Mace Ta Farko Da Ta Yi Alkalanci A Wasan Nahiyar Afirka

Salima

Alkaliyar wasa Salima Mukansanga ta kafa tarihin macen farko da ta fara busa a gasar cin kofin nahiyar Afirka a karawar da Zimbabwe ta ci Guinea 2-1 a fafatawar karshe a rukuni na biyu ranar Talata.

Sai dai kuma Guinea ta kai zagaye na biyu duk da rashin nasarar da ta yi a hannun Zimbabwe, wadda ta yi ban kwana da gasar bana da ake yi a Kamaru kuma Zimbabwe ce ta fara cin kwallo biyu ta hannun Knowledge Musona da kuma Kudakwashe Mahachi.

Kyaftin din Guinea, Naby Keita ne ya zare daya a wasan da suka yi a Yaounde da alkaliya, Salima Mukansanga ta kafa tarihi a babbar gasar kwallon kafa ta Afirka da a yanzu ake bugawa a Kamaru.

‘Yar kasar Rwanda, mai shekara 35 ta zama macen farko da ta yi busa a gasar kofin Afirka tun da aka kirkiri wasannin sannan Guinea ce ta yi ta biyu a rukuni na biyun a kan Malawi ta uku, wad-da ta tashi wasa da Senegal ba ci.

Guinea za ta fafata da duk wadda ta yi ta biyu a rukuni na shida kenan ranar 24 ga watan Ja-nairy, ba tare da dan kwallon Liberpool ba, Keita wanda ya karbi katin gargadi biyu, zai yi hukuncin wasa daya kenan.

Mukansanga ta bayar da katin gargadi shida jumulla a wasan, wadda ta taba busa gasar kwallon kafa a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympic da aka yi a birnin Tokyo a bara.

Exit mobile version