Sallah: Ba Za Mu Yarda Da Badalar Kanawa Ba – Hukumar Tace Finafinai

Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano, ta gargadi al’umma da su guji yin abubuwan da ba su dace ba, a lokacin bukukuwan sallah a jihar, musamman yin cudanya tsakanin maza da mata. Sakataren Hukumar tace finafinai na Jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakalla ne ya bayyana haka a ranar Asabar a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin labarai na kasa a Kano.

Afakalla, ya bukaci masu shirya shagalin bukukuwan na Sallah,  da su guji gwamutsa maza

da mata a wuraren tarukan Sallah domin kaucewa faruwar abubuwan da ba su kamata ba. Ya ce hakkin Hukumar tace Finafinai ne, tabbatar da tsaftace wuraren gudanar da ire-iren wadannan taruka a lokacin bukukuwan Sallah.

“Ba za mu hana jama’a ci-gaba da gudanar da harkokin bukukuwan Sallah ba, amma dole ne mu tabbatar da ganin an samu da’a a dukkanin wuraren taruwar Jama’a.” Don haka ya tabbatar da cewa, Hukumar za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin wuraren bukukuwan Sallar sun kaucewa abubuwan da suka shafi rashin da’a  Jihar Kano”, in ji shi.

Exit mobile version