Sallar Layya: Yadda Barayin Raguna Suka Addabe Jama’a A Lokoja

Sallar Layya

Daga Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja

A ci gaba da shirye shiryen da al’ummar musulmi suke yi na hawan Idin babban Sallah, a gobe Talata, idan Allah Ya kaimu, wasu mazauna garin Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, musamman wadanda suka sayi raguna, a yanzu suna zaune cikin fargaba, duba da yadda satar dabbobi, musamman ma raguna ta zama ruwan dare a yankunansu.
Jaridar LEADERSHIP A Yau ta nakalto daga wasu mazauna yankin rukunin gidajen 200 Housing Units dake birnin na Lokoja, cewa a yanzu barayi na sace sacen raguna a gidaje daban daban dake yankin.
Hajiya Aisha Inusa Kadir, wacce mazauniyar yankin na rukunin gidajen na 200 ne, ta shaidawa wakilin Jariidar LEADERSHIP A Yau cewa ta farka daga barci, amma abin mamaki sai kawai ta ga katon ragon data saya naira dubu saba’in( #70,000) yayi batar dabo, lamarin data bayyana da cewa abin bakin ciki da takaici ne matuka.
A yayin da Hajia Aisha take bayyana damuwarta da kuma yadda ta rika fadi tashi wajen samun kudin data sayi ragon layya da aka sace mata, shi kuma mallam Tanke Idachaba, wanda lamarin mara dadi na satar raguna ta shafa, ya bayyana rashin jin dadinsa ganin yadda shima ragonsa na layya yayi batar dabon, inda ya shaidawa wakilimmu cewa a daren lahadi da misalin karfe 2 na dare, ya farka ya ga ragonsa na layya daya saya naira dubu dari da ishirin da biyar(#120,000) a daure, amma kuma abin mamaki, ya tashi da misalin karfe 5 na Asuba’i zai je masallaci, sai kawai yaga babu rago a turke.
Mallam Idachaba, wanda yace yanzu haka yana kokarin har hada kudi domin sayan wani ragon layyan, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro dasu kawo ma yankin dauki domin kaucewa ci gaba da faruwar hakan nan gaba.
Wakilimmu wanda ya zazzaga kasuwar sayar da dabbobi dake kauyen Okumi dake kusa da birnin Lokoja, ya nakalto cewa a yanzu farashin dabbobin na neman gagarar aljihun musulmi marasa karfi, domin kuwa farashin raguna sai hauhawa suke yi.
Farashin raguna a kasuwar dabbobin a yanzu sun kama daga naira dubu hamsin(#50,000) zuwa naira dubu dari biyu da hamsin(#250,000), kuma ana sa ran farashin zai karu gab da ranan Sallah, kamar yadda wani mai sana’ar sayar  da raguna a kasuwar dabbobi dake Okumi , Mallam Bala Mairago ya shaidawa wakilimmu.
Da yake zantawa da wakilimmu game da sace sacen ragunan layyar, wani malamin addinin musulunci dake birnin Lokoja, Sheikh Yahaya Salihu, wanda har ila yau limamin masallacin juma’a ne a garin na Lokoja, ya gargadi musulmi dasu guji yin amfani da kudaden haram wajen sayan rago domin yin layya,inda yayi nuni da cewa Allah( SWT) tsarkakakke ne kuma Yana amsar tsarkakakken abu ne kawai.
Sheikh Salihu har wa yau, ya shawarci musulmi dasu sanya kyakkyawan niyya wajen yin layya domin kuwa yana daya daga cikin sharudodi da kuma ka’idojin karbabbiyar layya.
Malamin addinin musuluncin, kazalika ya kara da cewa jinin ragon na layya bai kai darajar tsarkin zuciyar wanda yayi layyar ba.
Ya kuma yi bayanin cewa yanka dabba a matsayin layya yana da muhimmanci da kuma dimbin lada, amma idan aka yi shi da kyakkyawar niyya.wanda ake yinsa a ranan 10 ga watan Zulhajji da kuma kwanaki uku na gaba.
A kan haka, Sheikh Salihu ya bukaci musulmi wadanda Allah Ya horewa abin yin layya dasu tabbatar dabbar da zasu yanka ya kai shekarun da ake bukata,inda ya kara da cewa a kalla rago ko tunkiya ya kai watanni shida, akuya mai shekara guda, saniya mai shekaru biyu, sai kuma rakumi mai shekaru biyar.
A karshe, malamin addinin musuluncin yayi kira ga musulmi dasu ji tsoron Allah a dukkan al’amuransu na yau da kullum.
A yanzu dai wasu mazauna garin Lokoja, wadanda suka zanta da wakilimmu sun ce daga yanzu har zuwa ranan Sallah, zasu rika sanya ido a dabbobinsu na layya, suna mai cewa  idan suka yi sakaci, sai dai suji ana layya a wasu gidajen, ganin cewa wasunsu basu da kudaden sake sayan wani dabbar duba da matsin tattalin arziki da kasa ke ciki.

Exit mobile version