- Yana Dab Da Kawo Sauyi A Harkokin Noma Kafin Ya Rasu – Ogbeh
Daga Nasir S. Gwangwazo,
An kammala bikin jana’izar Shugaban Gungun Kamfanonin Jaridar LEADERSHIP, Marigayi Sam Nda-Isaiah, a jiya Litinin. An binne gawar tasa ne a kabarinsa da ke makabartar Gudu a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya da ke Abuja.
Nda-Isaiah, wanda shi ne mamallakin jaridun LEADERSHIP, NATIONAL ECONOMY da kuma jaridar Hausa ta farko a tarihi mai fitowa kullum, wato LEADERSHIP A YAU, ya rasu ne a ranar Juma’a, 11 ga Disamba, 2020, da daddare bayan jaeriyar rashin lafiya.
An gudanar da addu’o’in neman gafarar Allah ga mamacin tare da bin ka’idojin Annobar Korona, kamar yadda sharuddan Gwamnatin Tarayyar Nijeriya su ka gindaya.
A cikin wadanda su ka halarci jana’iza akwai tsohon Ministan Gona kuma Shugaban Kungiyar Tuntuba ta Arewa, Malam Audu Ogbeh, Wakilin Babban Hafsan Sojojin Kasa, Manjo Janar H.I. Bature; Shugaban kamfanin TACK Agro And Chemicals, Mr. Thomas Etuh; na Ko’odinetan Kasa na Initiatibe for Peoples Rebirth (IPR), Manjo Janar Henry Ayoola mai ritaya da sauransu.
Lokacin da ya ke magana jim kadan bayan kammala jana’izar ga manema labarai, Cif Audu Innocent Ogbeh ya bayyana cewa, gabain rasuwar ‘Uncle Sam’ (kamar yadda da dama ke kiran sa) ya na shirin aiwatar da wani gagarumin shirin noma da harkokin hada magunguna, wanda zai iya kawo sauyi a bangarorin.
“Duk lokacin da ya zo mu na magana ne a kan matsalolin kasar, fatanmu da burinmu da kalubalen da ke fuskantar kasar a yanzu da nan gaba, musamman ma kan batun da ya fi shafar tattalin arziki da siyasa.
“Sam Nda-Isaiah ya na da zuzzurfan tunani. Ya na sha’awa kan harkokin noma, wanda ni ma na ke da shi ta yadda har ma ya na shirin fadawa cikin wani gagarumin aikin noma da hada magunguna.
“An kafa kwamiti, wanda Shugaba Buhari ya sanya ni shugabancinsa, don tuntubar Indiya da Chana, don shigo da kayan aiki cikin kasar. Mu na aiki kan hakan kafin na bar gwamnati kuma mu na fatan cigaba da shi, amma ga shi wannan abin takaicin ya faru.
“Ba mu da ikon hana kaddarar Ubangiji. Kawai sai dai mu yi wa dukkan ’yan Nijeriya godiya bisa nuna damuwarsu kan wannan rasuwa, kuma mu yi addu’a ga iyalin mamacin da jaridar LEADERSHIP,” in ji Ogbeh.