Daga Idris Aliyu Daudawa,
Idan Allah ya kaimu gobe Litinin za a yi jana’izar marigayi mawallafin jaridar LEADERSHIP Sam Nda-Isaiah a makabartar Gudu da ke Abuja babbar birnin tarayya Abuja, da karfe goma na safe kamar dai yadda iyalansa suka bayar da sanarwa. Sam Nda-Isaiah da ya rasu ne da daren ranar Juma’a 11 ga watan Disamba 2020.
Za ayi Jana’izar rufe shi ne bisa su ka’idojin hana yaduwar Cutar Korona kamar yadda kwamitin babban birnin tarayya ya bada sanarwa, ko kuma yadda aka sani tun lokacin da annobar ta bulla a Nijeriya, sai kuma wanda aka gaiyata ne kawai ake sa ran ya je wurin.
Mista Sam Nda-Isaiah ya shahara kwarai wajen taimakon al’umma ga kuma iya sanin yadda zai zauna da mutane da basu shawara ta gari, mai son hadin kan ‘yan Nijeriya ne, kamar dai yadda wasu abokan makarantar sa, kungiyar hada magunguna ta kasa, abokan huldar sa na siyasa, da dai sauran mutane suka bayyana lokacin ta suka zo yin ta’aziyyar sa.
A yau Lahadi ne ake gabatar da adduo’I da wakoki ta musammam a coci don ban kwana da shi.