Mamuda Abdullahi Indabawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Sam Nda-Isaiah: Ba Rabo Da Gwani Ba

by Mamuda Abdullahi Indabawa
December 20, 2020
in LABARAI
5 min read
Sam Nda-Isaiah
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Malamai suna gaya mana cewa duk lokacin da wata annoba ko masifa ta sameku to ku yawaita fadar wannan kalma saboda haka rasuwar Mai Gidan mu watau MR. SAM NDA ISAIAH itama annobace ko masifa ce a gurin dukkanin mutanan da suke da sha’awar karance – karancen rukunan jaridun da kamfanin jaridar LEADERSHIP suke wallafawa musamman rubuce-rubucen shi MR. SAM NDA ISAIAH yake yi a zato ma wammam damuwa ko ince tashin hankali mu marubuta na qungiyar mjalisar (Burin Zuciya) mu zamu fi kowa shiga cikin damuwa da wannan rashi.

Inna da dalilai masu tarin yawa da suka sa na fadi haka, amma kafin hakan zan bayyana yadda na ji lokacin da na sami labarin rasuwar ranar 12/12/2020 da misalin karfe shida na safe sai na ji waya ta tana kadawa inna dagawa sai naji muryar Malam Sani Rogo Aikawa mun gama gaisuwa sai yace dani kasami labarin rasuwar Mai Gida mu MR. SAM nan da nan kuwa na ambaci waccan kalma dana fara amfani da ita a farkon wannan ta’aziya tawa har sau uku daga nan nace wa Sani Rogo Allah ya bamu juriya da hakurin wannan rashi tun lokacin da Sani Rogo ya sanar dani rasuwar nan sai na ka sa yin komai na dau lokaci mai tsawo inna ta jimamin abinda ya faru haduwata ta farko da MR. SAM shine a Kaduna gidan “AREWA” lokacin da aka yi wani taro, bayan an tashi daga taron ne sai na matsa kusa dashi na gabatar masa da kaina nan take yace aiya dade sanin fuska ta amma a shafin jaridu sai yau ya ganni ido da ido sai nace ranka ya dade amadadin dukkanin mambobin majalisar “BURIN ZUCIYA” da suke a “NIJERIYA JAMHURIYYAR NIJAR, DA GHANA DA SHUDIARE BIYA” ni shugaban qungiyar muna godiya da ake bamu kyauta a shafin jaridar LEADERSHIP HAUSA sai yace dani chayaman ba komai ai taimakon juna muke da ku mukeyi domin rubuce-rubucan da kuke yi suna kara mana yawan makaranta jaridar.

samndaads

Sai haduwa ta dashi ta biyu itace a shekarar “2015” lokacin da ya fito takarar shugabancin kasar nan, da muka ji labarin ta wagar sa zata ziyarci Kano sai ni da Malam Sani Rogo Aikawa muka umarci mambobin mu maza da mata duk na kananan hukumomin Jahar arba’in da hudu “44” muka taro shi tun daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano har zuwa dakin taron watau gidan “MAMBAIYA” na Malam Aminu Kano mun yi kokarin samun hula hana salla da bajo da yake cewa mu yan qungiyar majalisar Burin Zuciya ne bayan kowa ya gama jawabinsa shi uban  gayya watau MR. SAM a cikin nasa jawabin ne yake cewa yana godiya da yan qungiyar Burin Zuciya abin da ya gani da idansa ba labari aka bashi ba ya burge shi kuma ya da tawa taron armashi sosai, bayan an tashi daga taron ya kirani yace chayama nace ranka ya dade kaga anan ba za mu samin damar tauna komai ba saboda yawan jama’a amma  nan gaba zan kiraku Abuja ko Kaduna inda zan yi muku godiya ta musamman nace Allah ya kaimu mu ka raka shi ya bar Kano. Wanda har yau dinnan ba mu yi wannan zama da shi ba, muna zaton akwai dalilai kamar hudu ko uku wanda suka hana wannan zama  a tsakaninmu mu san guda biyu daga cikin su, amma tun da ba to nan silili ko fasa bara gurbi kwai muke yi ba ta’aziyar da alhinin rasuwar mai gidanmu muke yi a rufe shafin.

Haduwa ta dashi ta uku itace lokacin da zai qaddamar da takararsa amina idan NEJA kowanne dan takara yana tafiya Abuja don qaddamar da takararsa amma shi MR. SAM sai ya zabi ya qaddamar da nasa a garinsu Amabaifarsa watau Mina Babban Birnin Jahar NEJA burin ko wane dan siaysa ace ya fara karbuwa a mahaifarsa, da muka ji wannan shirye-shirye sai mu shugabanni muka hadu da madugun majalisar tamu watau Al’amin Ciroma muka baiwa mambobinmu shawara da suke kusa da Jahar NEJA wanda yaga zai iya da kudin mota da gurin kwana da abinci muna bukatar mu hadu amina haka ake yi akalla mun samu wakilcin jihohi Kano, Katsina, Kaduna, Nasarawa, Fulato, Neja, Bauchi, Jigawa, Abuja da dai sauransu, mun hadu a filin inda nan ma muka samar da hula hana salla da bajo na ratayawa a wuya duk inda muka shige a wajen taron an san mune, a cikin tsare-tsaren mu yan Burin Zuciya bama cikin wadanda aka shirya za su yi magana, amma saboda mun burgeshi sai yace a gayawa mai gabatarwa daya daga cikin mu shima ya hau doro yace wani abu, saboda haka sai shwara ta fada kaina cewa ni zan yi magana amadadin kowa da kowa da M/C ya kirani aka fada masa suna sai na sami kaina a tsaka mai wuya watau gaba kura baya damisa, dalili a lokacin daban kenan da ahalin yanzu da nake yin wannan ta’aziya ni gangariyar don jam’iyar “P.D.P” ne domin in na rike da shugabancin dattawan jam’iyar a mzabata ta Kofar Dan’agundi dake Kano, ka ga kenan ni dan adawa ne ga jam’iyyar “NPP” da ake san na yi magana.

Ba nufina bane cikin wannan ta’aziyya na fada tarihin rayuwa, karatu, aikace-aikacan shi Mr. Sam ba illa abu daya kawai zance anan, watau kamar yadda Marigayi Dr. Mamman Shata Katsina ya fada a cikin wakarsa ta bakandamiya inda yake cewa bai gaji roko, kida da waka ba, amma ya shigo rana tsaka ya gagari ‘ya’yans gado, to haka shima Mr. Sam duk da cewa ya gaji aikin jarida a wajan mahaifinsa don nasan lokacinsa ya keyin aiki da jaridar Triumph Mallakar gwamnatin kano amma shi Mr. Sam dukkan karatunsa akan mai hada magunguna yayi su watau “famasi” saboda jinin aikin jarida da yake a jikinsa, rana tsaka ya shigo harka ya gagari yan’uwansa da suka gada da ma yan mun hauro ta kan katanga wadannan dama ba sai an fada ba diban karan mahaukaciya yayi musu misali mu dauki Gwamnatin Olusegun Obasanjo yana daga cikin yan jaridar da suka tsokanewa gwamnatin idanu musamman hawa na biyu da lokacin TAZARCE mu yan NIJERIYA shaida ne na irin gwagwarmayoyi da jama’ar gwamnati.

Saboda haka anan zan yi amfani da wannan dama na yi kira ga Gwamnatin Mai Girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta sami wani guri a cikin garin Abuja ta sa sunan MR. SAM NDA ISAIAH don tunawa da shi saboda mun san yana daya daga cikin manyan mutane da suka taimaka wajen hawan Buhari kan kujerar shugabancin kasa, ko kuma ita Gwamnatin NEJA tasa sunansa a wani katafaren guri na gwamnati. Haka ma zan sake amfani da wannan dama na yi kira ga shugabannin wannan kungiya tamu  mai albarka ta Burin Zuciya musamman shugaban da yake riko tun da ba’a yi zabe ba watau Mustapha Mando Dankasa kayi kokarin tuntubar wadannan mutane don dawo da ruhin tafiyar kamar da, madugun majalisar Al’amin Ciroma Kaduna, Alhaji Habibu Malele Jos, Sani Rogo Aikawa Kano, Alhaji Murtala Mai Salla Kano, Amina Waziri Kaduna, Surajo Almustapha Sokoto, Mai Unguwa Bello Dandin Mehe Suleja Neja, Usman Bauci, Alhaji Zakari Zanwan Lafiya Nasarawa, Haruna lifton Kaduna, Alhaji Garba Gololo Bauchi, Hamza Sa’idu Abuja, Yusuf Lado Katsina, Isma’ila Sanyantis Katsina, Alhaji Auwalu Azare Agege Lagos, idan ka tuntubi wadannan mutane dama wadanda zasu tsara maka tafiya bisa kan hanya.

Daga qarshe, amadadin dukkan mamba na wannan zaure na muna mika ta’aziyyarmu ga iyala, yan’uwa, abokai da ma’aikata na shi Mr. Sam Allah ya bamu hakurin juriyar rashin da muka yi.

Mamuda Abdullahi Indabawa

Shugaban Kwamitin Amintattu

08055101909

 

SendShareTweetShare
Previous Post

An Kaddamar Da Aikin Gundumomin Kidaya A Kananan Hukumomin Jihar Kano

Next Post

An Nemi Gwamnatin Katsina Ta Samar Wa Kungiyar Masu Kayan Marmari Fili A Garin Funtuwa

RelatedPosts

Zaben Dan Majalisa

Za A yi Zaɓen Gwamnan Anambara Ranar 6 Ga Nuwamba – INEC

by Mamuda Abdullahi Indabawa
4 hours ago
0

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar...

Ogun

Fashewar Tankar Mai Ya Ci Rayuwar Mutum Uku Da Jittaka Shida A Ogun

by Mamuda Abdullahi Indabawa
11 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, A ranar Talata ne mutum uku...

Bafarawa

’Yan Nijeriya Sun Fi So A Magance Rashin Tsaro Fiye Da Korona, Cewar Bafarawa

by Mamuda Abdullahi Indabawa
11 hours ago
0

A Juya Kuɗin Rigakafin Cutar Naira Biliyan 400 Zuwa Tsaro...

Next Post
Kayan Marmari

An Nemi Gwamnatin Katsina Ta Samar Wa Kungiyar Masu Kayan Marmari Fili A Garin Funtuwa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version