Daga Bello Hamza,
Sakataren gwamnantin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana marigayi shugaban kamfanin LEADERSHIP Sam Nda- Isaiah a matsayin abokinsa na hakika wanda ya tsayu wajen fadin gaskiya.
Sakataren gwamnatin ya bayyana haka ne a ziyarar ta’aziyyar day a kai gidan marigayin, ya kuma kwamitin shugaban kaa kan cutar koroina ta samu goyon baya matuka daga marigayin.
A ta’aziyyar day a gabatar, ya kuma ce, marigayin mutum ne yak e fadin zuciyasa ba tare da boye gasikiya musamman akan abin ya shafi ci gaban al’umma.
Ya kuma kara da cewa, “Mutum ne day a yi rayuwa tare da tabbatar da gaskiya ya kuma yi fafutukar neman na kansa, wannan na daga cikin daliln da suka say a samu gaggarumar nasara a kusan dukkan harkokin day a fuskanta a rayuwarsa, tun daga rubutun a jarida har ya zuwa yadda ya mallaki hamshakin gidan gada labarai a kasar nan.
“Sam abin koyi ne wanda taimaki al’umma da dama a rayuwarsa, tabbas an yi a sararsa a bangaren yada labarai a kasar nan.
“Sam aboki na ne wanda nake mutuntawa matuka, yana fadin gaskiya komai dacinta, kuma zan yi kewar shawarwarinsa a gare ni. Sam mutum ne mai sauraron duk mastalolin da ka fuskance sad a ita.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma ba iyalansa hakurin jure rashin.