Daga Idris Aliyu Daudawa,
Mambobin shugabannin First Bank sun bayyana cewar rayuwar marigayi shugaban kamfanin jaridar LEADERSHIP Sam Nda- Isaiah ya yi rayuwa wadda take tattare da abubuwan da za su amfani al’umma.
Wadannan bayanan suna cikin takardar ta’aziyya ga su iyalan mawallafin wadda kuma take dauke da sa hannun shugaban sashen kasuwanci da al’amuran sadarwa na Bankin Folake Ani- Mumney.
Wasikar ta bayyana su abubuwan da Sam ya bari wasu hujjoji ne wadanda suke nuna bambancin a bayyanae yake, idana aka yi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar, ta bangaren aikin jaridar da kuma ci gaban kasa baki daya.