Shugabannin jami’ar Jos sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da rasuwar mawallafin jaridar LEADERSHIP Sam Nda Isaih, wadda suka bayyana cewar mutuwar ta zo ne lokacin da aka fi son amfani da gudunmawar kwarewarsa.
Sun bayyana cewar marigayi Sam Nda Isaih shararre ne a bangaren harhada magunguna, dankasuwa, dan siyasa, kuma shararren kwararren dan jarida.
Sun cigaba da bayanin cewar mu anan jami’ar Jos a cikin wasikar ta‘aziyyar da suka rubuta, wadda kuma mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Sabestine Maimako ya ce, shi marigayin koda yaushe bukatar shi ita ce, yana mai son yaga kasar Nijeriya tana tafiyar da harkokinta, kamar dai yadda ya dace a rika yi, inda kuma yake amfani da kafar watsa labarai ta jaridar sa ta Leardership wajen yada ita manufar tasa.
Mu anan jami’ar Jos munyi amfani da jaridar tta shi wajen yada manufofin namu, muna kuma saran yadda muka fara yin mu’amala ta taimakon juna da kuma zumunci hakan zai cigaba.