- Kungiyar Masu Hada Magunguna Ta Yi Ta’aziyya
- Ba Mu Yi Mamakin Nasararsa A Fagen Aikin Jarida Ba —Shugaban Jami’ar Christland
Gobe za a gudanar da addu’ar rasuwar Shugaban rukunin kamfanin jaridar LEADERSHIP, Sam Nda Isiah, wanda wanda aka dage aiwatar da shi a International Conference Center Abuja, biyo bayan sauyin da aka samu a jana’izar bisa bin umarnin gwamnatin tarayya na takaita taron jama’a saboda kiyaye dokokin Korona.
A sanarwar da ahalin marigayin suka suka fitar mai dauke sa hannun Abraham Nda Isaiah, ya ce an samu canjin ne bisa ga wasu dalilai daga gwamnatin tarayya na bin dokokin kamar yadda aka tsara
Yayin da suke nadamar duk wani abin da ya faru na rashin daidaituwar da ka iya haifar wa abokai da sauran masu fada a ji wadanda za su iya sanya wakoki cikin tsarin jadawalin su, dangin Nda-Isaiah sun nanata cewa canjin ya yi daidai da sabbin takunkumin da gwamnatin tarayya ta sanya don kare yaduwar cutar Korona.
Marigayi Sam Nda-Isaiah, mai shekara 58, ya rasu a ranar Juma’a, 11 ga Disamba, 2020 bayan gajeriyar rashin lafiya, za a yi masa a ranar Litinin, 28 ga Disamba, 2020 a makabartar Gudu, Abuja da karfe 10 na safe.
Marigayi Sam Nda-Isaiah, 58, ya rasu ranar Juma’a, 11 ga Disamba, 2020 bayan gajeriyar rashin lafiya, za a yi jana’izarsa ranar Litinin, 28 ga Disamba, 2020 a makabartar Gudu, Abuja da karfe 10 na safe.
Nda-Isaiah ya kasance masanin harhada magunguna, dan kasuwa, attajiri, kuma masani a fannin kafofin yada labarai, kuma hazikin dan siyasa wanda rasuwarsa ta haifar da tarin alhini.
a fadin kasar da kuma kasashen waje.
Knungiyar masu hada magunguna ta Nijeriya ta bayyana cewar marigayi Sam Nda Sam Nda-Isaiah a matsayin sa na kwararre da ya karanta yadda aka hada magunguna, gudunmwar daya bada ta shafi fannoni da yawa na rayuwa a Nijeriya da kuma wajenta.
Ab takardar ta’aziyyar da take da sa hannun shugaban kungiyar Farfesa Ahmed Tijani Mora, kungiyar kanta ta bayyana cewar shekarun da marigayi Sam ya dauka yana ayyuka raya kasa, da suka kunshi ganin cewar abubuwa suna tafiya cikin gaskiya da rikon amana, hakan ne ya say a kasance shugaban tawaga ba kamar yadda wasu suke ba.
Farfesa Mora ya kara bayyana rasuwar Nda-Isaiah’ wani babban rashi ne gare shi, da kuma iyalansa, saboda kuwa sun kasancewa ‘yan’uwa wadanda suke ba juna shawara ta musayar ra’ayi, da yake dukkan su kwararru ne ta dukkan wani sashe daya shafi hada magunguna da kuma harka da kashin kai. Ya kara da bayanin marigayi kuma mawallafi wani babban jami’i ne, da dukkan abokan aikin sa da kuma hulda suke ganin girman sa, kai har ma wadanda suke sdana’arsu ta zama kusan daya.
Yayin da take isar da gaisuwar ta’aziyyar kungiyar ga daukacin iyalan marigayin, tayi fatar Allah ya basu hakurin jure ita rasuwar, shi kuma marigayin Allah ya jikan Kakakin Nupe.
Ba muyi mamaki ba yadda ya kasance dan jaridan da ya samu babbar nasara – Shugaban jami’ar Christland
Shi ma shugaban jami’ar Chrisland Chinedum Peace Babalola a cikin na shi jawabin ta’aziyyar ta marigayi ya nuna jajantawarsa da alhinin sa akan rasuwar, ba abin mamaki bane a matsayinsa na kungiyar su ta masu harhada magunguna, sai kuma ya kasance mai babban kwazo a fagen aikin jarida.