Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
A bikini saukar Alkur’ani Karo na goma na makaranatar Nurun Nabiyi dake Sabuwar Unguwa a Karamar Hukumar Kumbotso inda dalibai 70 suka Yi dacen Sauke Alkur’ani Mai girma, sannan Dalabai 25 daga cikin wancan adadi suka samu Haddar Alkur’ani Kamilan.
Shugaban makarantar Gwani Abdussalam Abdulkadir ne ya bayyana haka Alokacin da yake gabatar da jawabinsa. Bayan tabo dogon tarihin Makarantar, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda a tsakanin shekara goma Dalabai sama da 360 makaranatar tayi bikin shaida saukar su tare da samun Hafizan Alkur’ani masu yawa daga cikin wannan adadi.
Da ya ke gabatar da jawabinsa Alhaji Abdullahi Namama Dan Majen San Turakin Ringim ya jinjinawa kokarin malaman wannan Makaranta Wanda yace duk nasarar da aka samu ta biyo bayan sadaukar da kansu ne. Don Haka sai ya jakunnen dalban da suka samu wannan baiwa daga da cewa su dauka yanzu suka fara neman ilimi.
Alhaji Namama ya jadadda aniyarsa na ci gaba tallafawa irin harka ta Alkur’ani aduk inda aka bukaci hakan, daga Nan sai ya bukaci al’umma su kara jajircewa wajen gudanar da addu’o’in neman dorewar zaman lafiya a Jihar Kano da Kasa baki daya.
Shi ma a nasa jawabin, Dallatun Kano, Alhaji Bashir Mahe Alu Wanda shima Tsohon dalibin wannan Makaranta ne, ya bayyana farin cikinsa bisa ganin wannan muhimmiyar rana, daganan sai ya taya daliban da suka sauke Alkur’anin murnar wannan abin alhairi.
Cikin wadanda suka gabatar da jawabai alokacin bikin saukar, akwai Gwani Yusif Isyaka Rabiu, Sakataren ilimin Karamar Hukumar Kumbotso Alhaji Hussaini Baba da sauransu.