Connect with us

LABARAI

Sama Da Jami’an NIS 3,548 Sun Samu Karin Girma

Published

on

Shugaban Hukumar Shige da Fice ta kasa (NIS) CGI Muhammad Babandede ya umurci a fitar da jerin sunayen kananan jami’an da aka kara musu girma a hukumance, tun daga kan masu mukaman I.A3 zuwa masu mukaman Sufeta (I.I) da kuma wadanda aka daga darajarsu zuwa mukaman C.I.A.

Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadin nan wacce ta yi bayani dalla-dalla a kan yawan wadanda aka yi wa karin girma a kowane mataki, ta ayyana cewa akalla jami’ai dubu uku da dari biyar da arba’in da takwas (3,548) ne suka samu karin girman.
Sanarwar ta ce ana shawartar jami’an da abin ya shafa su tuntubi sashen kula da ma’aikata na sassan da suke aiki domin ganin jerin sunayen da aka fitar.
CGI Babandede ya taya jami’an murna bisa kwazon aiki da suka nuna tare da biyayya wadanda suka kasance ma’aunin da aka yi amfani da shi wajen kara musu girma.
A wani labarin kuma, reshen NIS na Jihar Kwara ya kara samun karfin aikin sintirin da yake yi sakamakon kaddamar da karin sansanin jami’ai da Shugaban hukumar, CGI Babandede ya yi a Kuta da ke Jihar Kwara, inda hakan ya kawo adadin wadannan sansanonin a fadin kasar nan zuwa 13.
A yayin kammadarwar, CGI Babandede wanda mukaddashiyar jami’ar kula da shiyya ta hudu ta hukumar kuma har ila yau kwanturolar Jihar Kwara, Misis Edith Onyemenam ta wakilta, ya bukaci jami’an hukumar su kara kaimin aiki domin hana bakin-haure tuttudowa cikin kasar nan ta mashigin Kwara tare da saka kokarin gwamnatin tarayya wajen samar da motocin sintiri, kayan aiki da sauran kayan fasaha na zamani da aka amince wa hukumar ta yi aiki da su domin kula da iyakokin kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: