Connect with us

RIGAR 'YANCI

Sama Da Mutane Miliyan Guda Suka Nemi Aikin N-Power Cikin Awa 48

Published

on

Shafin hukumar daukan ma’aikata na shirin nan na gwamnatin tarayya mai suna, N-Power wanda aka bude ya sami halartar mutane sama da miliyan guda da su ke neman a dauke su aikin a cikin awanni 48 kacal.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a dauki mutane 400,000 ne a kashi na uku na shirin na N-Power.

Ma’aikatar ayyukan jinkai da abin da ya shafi annoba, ta fara shirin daukan ma’aikatan a kashi na uku na shirin na N-Power tun daga ranar 26 ga watan Yuni.

Ma’aikatar ta bayyana cewa shirin zai samar da ayyuka ga matasan Nijeriya a bisa mahangar nan ta shugaba Buhari ta aniyar fitar da mutane milyan 100 daga kangin talauci a kasar nan.

Bayanin halin da ake ciki a kan shirin daukan ma’aikatan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a Abuja ranar Lahadi da dare, wacce mataimakiyar daraktan yada labarai na ma’aikatar, Rhoda Iliya, ta fitar.

Sanarwar na cewa: “a bisa shirin nan da ya ke gudana a halin yanzun na rajistan masu sha’awar aikin shirin N-Power wanda aka fara yin rajistansa a daga ranar Juma’a, 26 ga watan Yuni, ta yanar gizo, ma’aikatar kula da ayyukan jinkai tana shaida cewa ya zuwa yanzun sama da mutane milyan guda ne suka nuna sha’awarsu na shiga cikin shirin ta hanyar yin rajistan sunayensu daga sassan kasar nan a cikin abin da ya gaza awanni 48 da bude shafin yin rajistan.

“Ma’aikatar tana nanata cewa duk wasu matasan Nijeriya da su ke a tsakankanin shekaru 18 zuwa 35 masu ilimi da ma marasa ilimin duk suna iya rubuta bukatarsu ta neman a dauke su a sabon shirin aikin wanda a wannan karon zai mayar da hankali ne sosai a fannin noma.

Ma’aikatar ta yi alkawarin yin adalci a wajen zaban wadanda za a dauka din, ta kara da cewa komai za a yi a shirin za a yi shi ne tare da al’umma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: