Connect with us

LABARAI

Sama Da Mutum 30,000 Ke Dauke Da Korona A Nijeriya

Published

on

Hukumar Kula da Cututtutaka NCDC a jiya Laraba Ta Bayyana Cewa A Yanzu akwai kimanin mutum sama da 30,000 dake dauke da cutar, sannan mutane 684 sun ruga mu gidan gaskiya.

Hukumar tace a jiya 8 ga Yuli, akwai mutane 460 dasuka kamu da cutar a inda mutane 15 suka rasu.

A yadda lissafin yake: An tabbatar da masu dauke da cutar sun kai 30,249. Mutane 12,373 Sun warke, sai Mutane 684 da suka rasu a fadin tarayyar Nijeriya.

Wadanda suka kamu da cutar a 8 ga Yuli sun kai 460 daga jihohi a 21, gasu kamar haka:
Lagos (150); Rivers (49); Oyo (43); Delta (38); FCT (26); Anambra (20); Kano (20); Plateau (18); Edo (14); Bayelsa (13); Enugu (13); Osun (12); Kwara (10); Borno (8); Ogun (7); Kaduna (6); Imo (4); Bauchi (3); Gombe (3); Niger (2) da Adamawa (1).
Advertisement

labarai