Daga Yusuf Shu’aibu
Sama da mutane dubu 100,000 ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Binuwai, sakamakon ruwan sama mai karfi da aka samu a yankin a cikin ‘yan kwanakin nan.
Mafi yawa daga cikin mutanen da ambaliyar ta shafa na zaune ne a Birnin Makurdi, fadar gwamnatin Jihar ta Benue, yayin da jami’an hukumar agajin gaggawar ta kasar wato NEMA ta fara aikin isar da kayayyakin jin kai domin jama’a.
A shekarar nan ta 2017 dai an samu ambaliyar ruwa a jihohi da dama na yankin arewa ta tsakiya da wasu sassan kasar nan.