Sama Da Mutum Dubu 100,000 Ne Ambaliyar Ruwa Ya Shafa A Binuwai

Daga Yusuf Shu’aibu

Sama da mutane dubu 100,000 ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Binuwai, sakamakon ruwan sama mai karfi da aka samu a yankin a cikin ‘yan kwanakin nan.

Mafi yawa daga cikin mutanen da ambaliyar ta shafa na zaune ne a Birnin Makurdi, fadar gwamnatin Jihar ta Benue, yayin da jami’an hukumar agajin gaggawar ta kasar wato NEMA ta fara aikin isar da kayayyakin jin kai domin jama’a.

A shekarar nan ta 2017 dai an samu ambaliyar ruwa a jihohi da dama na yankin arewa ta tsakiya da wasu sassan kasar nan.

 

Exit mobile version