Connect with us

LABARAI

Sama Da Yara 10,000 Suka Amfana Da Maganin Zazzabin Cizon Sauro A Adamawa

Published

on

Jihar Adamawa ta kaddamar da yaki da zazzabin cizon sauro karo na farko ga al’umman Karkara cikin watan da yagabatane aka kaddamar da shirin wanda ya shafi kananan yara ‘yan kasa da shekaru uku zuwa biyar.

Kimanin yara sama da dubu goma ne suka amfana da wanan shirin da aka yi a kauyukan ake cikin kananan hukumomin Michika Karamar hukumar Mubi ta Kudu da kuma Mubi ta Arewa.

Shirin da aka kaddamar da shi kyauta saboda tallafawa al’umman Karkara marasa galihu da annubar cizon sauro ke addabarsu.

Shirin rigakafin an yi shi ne domin ya zama garkuwa ga zazzabin cizon sauron  saboda illar da cizon sauraon ke janyowa a yanzu.

Bayan samar da kayayyakin inda aka horas da ma’aikatan da za su zaga kauyuka da suka hada da Rugan Fulani da kauyukan manoma  da sauransu ta yadda za’a samu nasarar yiwa yara wanan rigakafin. Wanda Hukumar kula da harkokin kiwon Lafiya ta duniya ke jagoranta.

An yi wa yara kanana allurar da kuma bada magani da raba gidan sauro wanda zai kare Lafiyar jiki lokacin da ake barci. Bayan raba kayan tallafin na zazzabin cizon sauron mun koyar da kimanin mutum 620, hanyoyin taimakawa wadanda suka kamu da irin zazzabin.

Sannan an wayar da kan  Sarakuna da Malaman addinai da Shugabannin kabilu ta yadda za su ja kunnin al’ummansu saboda kawar da abubuwan dake janyo sauro cikin jama’a.

Jihar Adamawa tana daya daga cikin Jihohin Arewa ta gabas wadanda suke fama da irin wannan matsala. Amma sakamakon gudanar da wanan shiri ta hukumar kula da kiwon Lafiya ta Duniya  ya sanya ana ganin an samu sauki fiye da kashi 46%.

Haka kuma an gargadi al’umma da su daina amfani da abubuwan kazanta kamar shaya da zubar da gurbataciyar ruwan da abubuwa mara amfani wadanda ke kawo sauro da sauransu.

Kwamishinar kiwon Lafiya ta jihar Adamawa Dakta Fatima Atiku Abubakar ta ce ; a shekarar 2017 kimanin mutum kashi 70% da suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro wanda yawansu yakai 850,000 aka sarinsu matane da yara kanana.

Ta ce; cutar ta yi masu illa ta yadda da yawa sun hallaka a sakamakon wanan cutar. Cutar zazzabin cizon sauro ta fi bada karfi ne a yankin Michika da Mubi  musamman ga al’ummar dake rayuwa a Karkara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: