Daga Ibrahim Ibrahim
A ci gaba da taimakon matasa da ya dade yana gudanarwa, domin ganin suna samun aikin da za su rika dogaro da kansu, babban kamfanin hada-hadar kimiyyar zamani da ke Arewa, wato Kamfanin Bizi Mobile Cashless Consultant Limited, zai dauki akalla Mata 500 wadanda suka kammala karatun Jami’a aiki, domin horar da su ilimi a kan abin da ya shafi hada hadar kudi irin ta zamani, wanda a turance ake kira da ‘financial inclusion’.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban Kamfanin Bizi Mobile Cashless Consultant Limited, Alhaji Aminu Aminu Bizi, a yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Kano, dangane da yadda kamfaninsa ya ke kan kudirin daukar Mata 500 wadanda suka kammala karatun Jami’a, amma babu aikin yi, wajen ganin kamfanin ya horar da su akan abin da ya shafi ilimin hada hadar kudi irin ta zamani wanda a turance ake kira da financial inclusion.
Alhaji Aminu Bizi, ya ci gaba da bayyana cewa, akwai tarihin Mata masu yawa wadanda suka dade da kammala karatun Jami’a amma babu aikin yi, suna nan zaune a gaban iyayensu, wasu kuma sun dade shekara da shekaru da yin aure har amma basu sami aikin da zasu dogara da kansu ba, wasu daga cikinsu sun tsaya jiran aiki daga bangaren Gwamnatin, wasu kuma tunanin yadda zasu tashi su dogara kansun ma bai zo masu ba.
A cewar sa, daga cikin ayyukan da za’a horar da su, sun hada da, bude asusun ajiya na bankuna, katin shaidar cire kudi na banki ATM, katin shaidar zama na Dan kasa, NIMC da dai sauran su.
Wanda a cewarsa, idan suka sami kammala wannan horo, kowacce daga cikinsu za ta kasance wakiliyar banki a gundumar unguwarsu, ma’ana, za ta zama tamkar bank agent, wacce za ta dinga wakiltar kowane nau’in banki da kake bukata domin ta bude maka asusun ajiya na bankin, sannan a nan take za ta baka katin ATM batare da jeka ka dawo ba.
Shugaban Kamfanin Bizi Mobile, ya kara da bayyana cewa, wadannan Mata zasu kuma kasance tamkar masu yin adashen gata ga kananan da manyan ‘yan kasuwa, ‘yan acaba, masu sana’ar kosai, waina, kanikawa, kafintoci da dai duk wasu masu nau’in sana’oin hannu.
Alhaji Aminu Bizi, ya ce, domin ganin ya zaburar da su, kamfaninsa zai yi amfani da nau’in kwamisho wajen biyan wadannan Mata ma’aikata albashi a ko wane sati ko wata wata, ya danganta da yadda kowacce takeso a biya ta hakkinta. A cewar sa, hakan zai zaburar da su wajen yin rige-rigen kwazon gasa a tsakaninsu. domin aikin zai kasance iya kwazon ka, iya albashin da kamfani zai biya ka.
Daga karshe, Shugaban Kamfanin Bizi Mobile, ya yi kira ga daukacin Matasan kasar nan musamman na yankin Arewa, da cewa lokaci ya yi, da zasu dawo daga rakiyar jiran aikin yi daga bangaren Gwamnatin, a cewarsa, idan dambu yayi yawa sam baya jin mai. Dole su mike su naimi na kansu, a cewarsa.