Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya, Dakta Ramatu Aliyu, ta yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan kirkirar shirin fadada Ayyukan Yada Labarai na musamman da nufin magance yawan marasa aikin yi a kasar. Mista Austine Elemue, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga ministar shi ta bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, a Abuja, ta yi wannan yabo ne a yayin bikin kaddamar da shirin a Jihar Kogi a filin wasa na garin Lokoja.
Ministar ta bayyana cewa, shirin shiga tsakani, wanda aka amince da shi a Oktoba na shekarar 2019 da aka aiwatar ga mutane 1,000 kowannensu daga kananan hukumomi 774 na kasar don yin aikin wucin gadi a lokacin rani.
Ramatu, wacce ta yarda cewa duk da cewa shirin ba sabon abu bane a Nijeriya, amma, ta ce wannan shi ne karo na farko da gwamnatin Nijeriya ta maida hankali kan ma’aikatan da basu da kwarewa.
Ta ce kafin yanzu, an fi mai da hankali ne ga wadanda suka kammala karatu marasa aikin yi da kwararrun ma’aikata.
“An kuma yi amfani da shirin yadda ya kamata a lokacin Afirka tana hannun turawan Mulkin Mallaka don saurin amsawa ga yanayi kamar fari da yunwa ta hanyar tattara mutanen da ba su da kwarewa don shiga cikin wasu manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a matsayin hanyar saukaka halin da suke ciki.
Shirin ba sabon abu bane ga Nijeriya kamar yadda Daraktan Ayyuka na kasa tare da hadin gwiwar Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO) suka fara gabatar da shi a tsakiyar shekarun 90s.
“Ko da yake, ILO da kanta ta samo ra’ayin Shirin Ayyuka na Musamman daga samfuran tarihi da yawa. Tun da farko, Malam Abubakar Fikpo, Mukaddashin Darakta-Janar na Ayyuka na Kasa, ya bayyana cewa shirin zai fara a watanni uku da suka gabata, amma abin takaici ya yi jinkiri saboda wasu lamuran da ba na dole ba.
Fikpo ya lura cewa tare da kaddamar da shirin, al’ummomin za su ga wata kwalliya ta hanyar wasu ayyuka na musamman da mahalarta za su yi tun daga aikin magudanar ruwa da kulawa da ciyayi, hanyoyin ciyarwa da sauransu.
Ya ba da tabbacin cewa an yi wa mahalarta tanadi yadda ya kamata kuma bankunan da aka kebe suka karbi bayanansu don ba da tabbacin ba tare da damfara ba, gaskiya da kuma samar da aikin adalci.
Mukaddashin Darakta Janar din, ya jaddada cewa domin tabbatar da sahihancin tsarin, an nada masu sa ido a dukkan mazabun kasar.