Connect with us

TATTAUNAWA

Samar Da Hukumar Kula Da Kwalejojin Kimiyya Zai Inganta Sha’anin Kere-Kere A Nijeriya, Inji Shugaban NAPS

Published

on

MOHAMMED SANI HASSAN Shi ne shugaban daliban kwalejojin kimiyya da fasaha ta Nijeriya a hirarsa da LEADERSHIP A YAU ya bayyana muhimmancin samar da hukumar da za ta kula da kwalejojin kimiyya da fasaha a Nijeriya, inda ya bayyana fa’idar da hakan zai kawo wa kasar nan, ya kuma yi tsokaci kan halin samun tallafin karatun dalibai a halin yanzu. KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi, ga hirar
Za mu so sanin da wanda muke tare?
Suna na Mohammed Sani Hassan nine shugaban dalibai na makarantun kimiyya da fasaha ta kasa, ‘National Association of Polytechnic Students’ ta Nijeriya gaba daya.

A daidai wannan lokacin me za ka iya shaidawa kan yanayin samun tallafin karatu ga dalibanku a fadin kasar nan?
Eh to, a kan hidimar tallafin karatu ‘scholarship’ akwai jahohin da gaskiya dalibanmu suna samun tallafin nan kuma suna amfana da su; amma kuma a wasu jahohi gwamnonin basu biyan wannan tallafin karatun, kuma wadanda basu biyan sun fi wadanda suke biya yawa. Bar na fara da jihar da na fito, jihar Bauchi kenan, zuwan gwamnati mai ci a karkashin gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar, gabanin ya amshi mulki gwamnatin baya ta tafi ta bar bashin ‘scholarship’ wanda ita gwamnatin baya bata karasa biya ba, zuwa M.A Abubakar ya biya sau daya tak, tun da ya biya wannan sau dayan bai sake biya ba, yau shekaru hudu kenan, sai kwana-kwanan nan ne aka fara saida ‘scratch card’ wanda yanzu haka ake kan saida shi wannan scratch card din ga daliban da za su ci sa’a ko za su samu tallafin karatun. Amma ni gaskiya zai iya danganta wannan da siyasa kawai, dalilina na fadin hakan shine kowa ya sani tallafin karatun nan duk shekara ne ake bayarwa, amma shekaru hudu gwamnatin da take kai bata biya ba sai sau daya, da lokacin zabe ya karato an fara yunkurin bayar wa daliban scholarship domin ganin siyasa ya kuma don gwamnatin ta zo karshe.
Abun da zan ce kafin na je wasu jahohin shine mu gaskiya a daina mana siyasa da hidimar daliban, duk da gwamnatoci daban-daban suna ta korafin rashin kudi amma ba zai iyu don lokacin siyasa ya zo ne kawai za a samu kudin da za a iya biyan daliban scholarship ba, wannan tamkar ana son amfani da dalibai ne kawai don zaben 2019.
Idan muka duba Borno, a Maiduguri dalibai sun shafe shekaru uku zuwa biyu basu samun tallafin nan, tun da shi wannan gwamnan ya zarce sau daya ya biya tallafin karatun. Gwamnan jihar Binuwai kam ma kwata-kwata baya biyan kudin scholarship na daliban jiharsa. Amma idan ka duba jihar Kano ita tana kokarin biyan tallafin karatu ga dalibai, jihar Jigawa ma tana kokarin biya, haka shi ma gwamnan jihar Nasarawa daliban suna shan wuya kan wannan tallafin kudin karatu ga daliban.
A takaice abun da nake son na fada maka a nan shine a Nijeriya muna da jahohi 36, amma a cikin jahohin nan, wadanda suke iya biya wa daliban jiharsu scholarship duk shekara-shekara basu wuce jihohi goma ba, kusan jahohi 26 basu ma damu da wannan lamarin na scholarship din ba.

Wasu wasu illoli da rashin samun scholarship ke janyowa ga karatu ne?
Suna nan da yawa, yanzu misali irin yawaitar shiga yajin aiki da ake yi duk basu wuce don karin kudin makaranta da sauransu; Makkon biyu da suka wuce kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Nasarawa na je makarantar a sakamakon kara kudin makaranta da shi Rector din yayi da kara wasu cajis wanda hakan ya janyo daliban suka ce sam basu yarda ba; wanda hakan har ta kai ga daliban sun yunkura don yin zanga-zanga, ina samun wannan labarin na je makarantar muka tattauna cikin ikon Allah aka sasanta. Maganar da na ke son na fitar a nan shine, idan gwamnati ba za ta bai wa dalibai scholarship ba, mene ne kuma na kara kudin makaranta? Ai saukin rayuwa ake nema idan an samu saukin rayuwa ne za ka ga dalibai sun yi karatu mai inganci don haka ina amfani da wannan damar wajen yin kira ga gwamnani su yi wa Allah suke taimaka wa dalibai domin yana taimaka mana gaya wajen kyautata karatunmu.

Idan muka juya gefe guda; me za ka ce kan banbance-banbancen da ake samu kan masu shaidar HND da masu Digiri?
Akwai wani zama da muka yin a gabatar da bayani nkan wannan lamarin, makkonni biyu sai gwamnatin tarayya ta bijiro da takarda kan cewar babu wani banbanci a tsakanin mai shaidar HND da mai Digiri domin an soke wannan banbancin. Sannan, har ga Allah a yanzu haka akwai wuraren da basu amfani da wannan banbancin, da mai Digiri da mai HND duk daya ne, amma har yanzu akwai wuraren da basu fara aiwatar da wannan umurnin ba. idan ka duba irin su Police, Army, Custom da sauransu ai duk HND da digiri daya ne a wajensu. An fi samun wannan banbancin a ma’aikatun jihohi, amma a bangaren gwamnatin tarayya an gyara matsalolin nan.

To yanzu mene ne ke ci muku tuwo a kwarya?
Ai mu yanzu ma haka muna so ne a samar da hukumar da za take kula da harkokin kwalejojin kimiyya da fasaha wato ‘National Polytechnic Commission’ ita wannan NPC ita ce za take ke kula da zallar harkokin kwalejoji a kasar nan, amma a yanzu haka polytechnics suna karkashin NBTE ne, alhali ita NBTE makarantun da suke karkashinta sun yi gayar yawa, a sakamakon yawansu hakan ya sanya ba a baiwa wasu wuri muhimmancinsu, amma idan aka samar da hukumar da za take kula da kwalejojin kimiyya da fasaha hakan zai kawo ci gaba, domin yanzu idan ka duba duk duniya ta ci gaba ne ta fuskacin kimiyya da fasaha, idan aka samar da wannan hukumar za ta zauna ta tsara yadda za a ciyar da kimiyya da fasaha gaba fiye da yadda ake kai a yanzu.
Ita wannan hukumar za ta zauna ne ta duba zallar kimiyya da fasaha domin a akwai wasu kwasa-kwasan da suke kwalejejin kimiyya da fasaha wanda a yanzu haka bai kamata a ce ana gudanar da su a cikin polytechnics ba; misali idan ka dauko irin su Public Admin, Business Admin, Mass Communication, da sauransu duk ya kamata ne a ce yanzu haka ana koyar da sune kawai a cikin jami’o’i, ita Poly ya zamana ana koyar da zallar kimiyya da fasaha ne kawai wannan zai kai ga inganta kimiyya da fasahar. Ya dai kamata gwamnati ta gyara tsarin gudanar da polytechnics, sannan kuma idan aka samar da wannan hukumar ya zamana sai a sauya ake koyar da digiri a maimakon HND, idan aka yi haka zai taimaka wajen kyautata ilimi a Nijeriya. Idan ka duba wannan HND kasashe da dama basu yinta, idan ka dauki takardar HND ka je da ita wasu kasashen basu santa ba, sai sun tuntuba kafin su gamsu, don haka idan aka soke HND aka dawo ana koyar da Digiri hakan zai kara kyautata sha’anin ilimi a fadin kasar nan, kuma kimiyya zai bunkasa hakan zai kai ga kawo ci gaban tattalin arzikin kasar nan, amma yanzu haka da jami’o’in da kwalejojin dukkansu ba baiwa sha’anin kimiyya muhimmanci ba, duk haka dole ne a dawo a duba a bata muhimmanci, domin kimiyya da fasaha ita ce ke sarrafa duniya don meye ba za a kyautata sha’anin kimiyya da fasaha a Nijeriya ba?, muna dai fatan gwamnatoci za su duba lamarin da idon basira.

Akwai wasu matsalolin da daliban jihar Bauchi ke fuskanta ne?
Daliban da suke karatu a kasashen waje suna cikin matsala gaya, domin gwamnati ta daina biyan tallafin da take basu. Daliban wadanda gwamnatin baya ta dauki nauyinsu, ita kuma wannan gwamnatin bata zo ta ci gaba da basu kulawa ba, yanzu haka akwai dalibai da dama suka dawo karatun ya gagara. Ka ga wannan babbar matsala ce, ita wata gwamnati ta rigaya ya dauki nauyin wasu dalibai ta fita da su kasashen waje, wata gwamnati taki kulawa da su hakan na jawo matsaloli, domin wasu daliban ba za su iya kaiwa ga kammalawa a sakamakon rashin kudade ba.

Daga karshe me za ka shaida a matsayinka na shugaban NAPS?
Ina amfani da wannan jaridar wajen yin kira ga ‘yan siyasa da suke tallafa wa dalibai, wasu ‘yan siyasa za su iya biyan tallafin karatu wa daliban a aljihunsu hakan zai rage wa gwamnati nauyin tallafin karatun dalibai. Kamar yadda na ce, a farkon hirarmu sam bai kamata ake amfani da hidimar dalibai wajen siyasa ba, muna jawo hankalin gwamnoni su ke tallafa wa dalibai yin hakan yakan kawo ci gaba wajen kyautata sha’anin karatu, kuma yana kara wa dalibai kwarin guiwar yin karatu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: