Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
HONORABUL YA’U UMAR GWAJO-GWAJO, shi ne tsohon Kakakin Majalisar dokoki ta jihar Katsina kuma shi ne shugaban kungiyar Manoma ta ‘Gaskiya Farmers’ ta Jihar Katsina, a zantawarsa da LEADERSHIP A YAU, ya bada shawara ga jama’a da su rungumi wannan jarida wacce ya ce ta kafa tarihi a duniya saboda yadda ta zama ta farko da take fitowa a kullum.
Sannan ya yaba da kokarin hukumar gudanarwa ta LEADERSHIP a kan yadda suka yi tunanin samar da wannan jarida mai fitowa kullum, inda ya ce hatta gwamnati a matakin jiha ko tarayya ba ta da wata jarida da ke fitowa kullum a yanzu.
LEADERSHIP A Yau: Honorabul me za ce ka game da wannan jarida ta LEADERSHIP da take fitowa kullum wanda kumaita ta faro a tarihin jaridun Hausa.
LEADERSHIP A Yau: Ganin cewa wannan jarida ta hausa ce wanda kuma mafi yawan al’umma musamman arewa da hausa suke magana me za ka ce game da haka?
Saboda haka samun wannan jarida ta LEADERSHIP A yau ba karamar hanyar ba ce ta sanin halin da shuwagabanni suke cikin ba, wanda hakan zai kara kawo wayewa a cikin al’umma. Musamman ganin cewa labarai sun kowa ta wannan hanyar, saboda haka ta nan ne mutun zai bi domin tallata hajarsa domin duniya ta sani, to jarida na daya daga cikin hanyar isar da wannan sako.
LEADERSHIP A Yau: Ganin cewa ita wannan jarida ta Hausa wane kira za ka ga jama’a domin su amfana da wanna garabasa ta zo ma su.
Honorabul Gwajo Gwajo: Kamar yadda na fada sha’anin harkar zamani da muke cikin shi ne ta wannan hanyar za ka bi domin isar da sakonka a ko’ina cikin duniya, za ka iya sanin halin da kasarka take ciki da halin da duniya take ciki da kuma uwa uba jahar da mutun yake. Saboda haka ina kira ga al’ummarmu su cigaba da sayan wannan jarida domin karantawa, sannan mu cigaba da bada tallace-tallacenmu.
Kamar yadda na ce yanzu wani yana da wata fasaha, acikin garinsu ko kuma kauyensu, amma duniya bata san wannan fasaha ta shi ba, sai kuma Allah Ya sa ga jarida mun samu kusa da mu, wanda za ta iya fadawa duniya abinda kake ciki. A matsayinmu na Hausawa ‘yan arewa mu kara mayar da hankali wajen sayan wannan jarida da kuma bada talla domin ta haka za ta bunkasa fiye da yadda ake tunani. Kuma ta haka za aiya jawo hankali jama’a domin su bada ta su gudunwa a kan wace irin harka.
Honorabul Gwajo Gwajo: Gaskiya ni a gareni tana daya daga cikin wanda za ta zama abin alfahari ga manoma domin kamar yadda na fadi, manoman nan Hauswa ne kuma ‘yan arewa ne, saboda haka wannan jaridar akwai rawar da za ta taka so sai akan sha’anin noma, kuma ina da tabbacin wannan jarida za ta taka rawa dari bisa dari akan sha’anin noma da kiwo, a wannan yanki na arewa da kuma kasa baki daya. Haka kuma ta wannan jarida ne manoma za su iya kai kokensu ga gwamnati sannan za su iya samun wani ilimi na musamman wanda ya shafi sha’anin kiwo da Noma.
Kuma za ta taka rawa wajen ganin manoma sun fahimce yadda za su kara inganta harkarsu ta noma. Kuma ta nan ne za su iya mika godiyarsu ga gwamnatin jiha ko ta tarayya ko kuma wata kungiya wanda ta kawo masu tallafi ko take son sayan wani amfanin goma.
LEADERSHIP A Yau: Ga su humumomin da suke buga wanna jarida wane kira kake da shi domin kara inganta
Honorabul Gwajo Gwajo: kamar yadda muka sani kowane irin al’amari kafin ya mike sai an sa hakuri, saboda haka su kara daukar hakurin na bullo da wannan shiri na jaridar LEADERSHIP A Yau, na san insha Allahu za a yi nasara akan wannan tafiya. Musamman yanzu babu wata jarida ta hausa mallakar gwamnati wanda ke fitowa kullum, to na san idan aka kara sa hakuri za a samu biyan bukata insha’Allahu. Kuma ina kara kira ga humumomin ita wannan jarida su kara tabbatar da cewa duk labarin da za su buga yana da inganci kuma na gaskiya ne, ba labarin kanzon kurege ba. Su kuma tabbatar sun tsare gaskiyarsu, wannan zai kara taimaka wajen samun nasarar wannan jarida.