Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
An yi kira ga gwamnatin tarayya ta hannun ma`aikatar gona ta tarayya da sauran hukomomi da suke da ruwa da tsaki akan bunkasa harkar noma a Najeriya, wanda gwamnatin Muhammadu Buhari ta ba mahimmanci a matsayin matakin farfado da tattalin arziki da ta wadata manoma da kayan aiki cikin sauki shi ne yafi duk wani shiri na ba manoma tallafi ko bashin noma a wannan kasa kuma a wannan lokaci.
Wannan bayyani ya fito ne daga bakin Mataimakin Shugaban Rukunonin Gamayya na Kamfanin Dangote Alhaji Sani Dangote a lokacin wani taro na bunkasa da kuma nona amfanin gona wanda kamfani buga Jaridar Daily Trust da hadin gwiwar ma`aikatar noma ta Jahar Kano ta gudanar na manoman Jahohin Arewa maso Yamma wanda aka gabatar a Kano.
Sani Dangote ya kara da cewa, idan aka wadata manoma da iri mai inganci da wadataccen takin zamani da kayayyakin noma kamar irin su motocin noma, maganin kwari da dai sauran abubuwa na noma su samu ga manoma cikin sauki, to yafi dukkan wani taimako da za ama manoma domin ta haka ne manoma zasu dogara da kansu kuma abinci ya wadata a same shi da sauki kuma su manoma su sami riba mai albarka.
Haka kuma ya ce mayan matsalolin su su ne rashin wadatattun madatsan ruwa wato Dam Dam dumin Dam daya kawai su ke da shi, domin haka suna bukatar madatsun ruwa fiye da yadda ake a yanzu, kuma babbar matsalar su ita ce rashin wadatattun kayan noma na zamani wanda ake amfani da su a Duniya.
Taron dai ya samu halarta mayan manoma da kanana da kuma kwamishinan aikin gona a Jahar Kano Honarabul Nasiru Yusuf Gawuna wanda yayi Dogon bayani akan yadda Kano ta yi wa Jahohi kasar fintinkau akan tsare tsaren aikin gona bisa samun goyon baya Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.