Daga Abubakar Abdullahi, Lafia
Kwamishinan ma’aikatar ilimin musamman, kimiya da fasaha ta Jihar Nasarawa Farfesa Jonathan Ayuba, ya kirkiro da kuma soma aiwatar da shirin bayar da abincin rana kyauta ga dukkanin wadanda ke aiki a ma’aikatar domin karfafa wa ma’aikatansa gwiwar aiki.
Kwamishinan wanda ya bayyana haka ga manema labarai a garin Lafia ya ce, za a rika bai wa kowane ma’aikacin ma’aikatar abincin rana kyauta na kwanaki uku a tsakanin ranakun aiki.
A cewarsa, daga yanzu a kashin kansa zai rinka bada abincin rana kyauta ga ma’aikatansa a ranakun Litinin da Laraba da kuma Juma’a a kowane mako.
Ta kwamishinan, “Dalilin samar da shirin shi ne, domin kara tabbattar da ma’aikatan ma’aikatar sun kasance tsintsiya madaurinki daya da kuma samar da wani dandali na tattaunawa da juna kan batuttuwan da za su kawo cigaba a ma’aikatar ba tare da la’akari da bambancin da ke a tsakanin ma’aikatan ba”.
“Muna amfani da lokacin cin abincin rana mu tattauna tsakanin babban sakatare da daraktoci da masu shara da direbobi. Idan aka samu kyakkyawar yanayin aiki da dangantaka mai kyau a tsakanin ma’aikata, aiki zai kara inganta”, in ji shi.
Har wa yau ya ce, an gyara da kuma inganta kayan aiki domin kara cusa wa ma’aikata sha’awar zuwa aiki. Dagan an, sai ya bayyana cewa gwamnati ta fara shirin daukar dalibai a makarantar nakasassu da ke Lafia da kuma malamai da za su karantar da su. Tare da cewa ayyukan gina makarantun nakasassu da a yankin Akwanga da Keffi sun yi nisa.
Ya bayyana cewa ilimin nakasassu a Jihar Nasarawa kyauta ne tun daga matakin firamari har zuwa makarantun gaba da sakandare, kuma da zarar sun kammala karatun gwamnati tana daukar su aiki.
A karshe, kwamishinan ya yi kira ga nakkasassu a jihar da su yi amfani da damar makarantunsu da gwamnatin jihar ta gina su nemi ilimi su kuma koyi sana’o’in hannun don amfanin rayuwarsu da kuma bunkasa tattallin arzikin jihar.