Connect with us

LABARAI

Samar Da Tashar Jiragen Ruwa A Cikin Teku Zai Bunkasa Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma— Hassan Bello

Published

on

An bayyana cewa, samar da tashar jiragen ruwa na zamani a can cikin
teku zai taimaka wa Nijeriya ta samu bunkasar tattalin arziki abin da
kuma zai matukar taimakawa harkokin zirga-zirgan ruwa a yankin Afrika
ta yamma da ma yankin Afrika gaba daya.
Shugaban hukumar Jiragen ruwa ta kasa, ‘Nigerian Shippers’ Council
(NSC)’, Mista Hassan Bello ya bayyana haka a tattauwarsa da manema
labarai, ya kuma ce, shirin samar da tashar jiragen ruwan ta cikin
tekun zai taimakawa harkokin fitar da kayyaki zuwa kasashen waje.
Bello ya kuma bayyana cewa, rashin zamanantar da harkokin tashoshin
jragenmu da rashin ingantaccen harkokn sufuri da kuma rashin aiki a
tashoshin jirahe uwa na tsawon awanni 24 na daga cikn matsalolin da
ake fuskanta a fagen harkar tashar jiragen ruwan kasar nan.
Ya kuma lura da cewa, mastalar annobar cutar korona ta fito da
matsalar dake fuskantar bangaren tashar jiragen uwan kasar nan, ya
kuma ce, hukumar NSC za ta hada hannu da sauran masu ruwa da tsaki a
bangaren don samar da mafita.
Ya ce, “Ina matukar farin cikn ganin zamu samar da tashar cikn teku
guda biyu a shekarar 2021 mai zuwa. Na ‘Ibom deep seaport’ da kuma
‘Lekki deep seaport’ tabbas za su samar da sabin yanayi da abubuwan da
za bunkasa tattalin arzikin kasar nan.”
“Samar da su zai taimaka mana mu cigaba da kasance jagora a bangaren
harkokin tashar jiragen ruwa a Afrika ta yamma. Za kuma mu tabbataar
da an samar da hanyoyin jiragen kasa da kuma samar da kayan aiki na
zamani don tafiyar da aikin yadda yakamata
An shirya tashoshin jiragen ruwan Nijeriya ne ta yada za su fitar da
kayyaki zuwa kasashen waje, amma a halin yanzu abubuwa sun canza dole
mu shirya fara fitar da kayyaki zuwa wajen kasar nan, don tattalin
arzikin duniya a halin yanzu ya danganta ne da yadda ake fitar da
kaya.”
Bello ya kuma ce, lokaci ya yi da gwamnati za ta inganta bangaren
harkokin sufurin ruwa don bunkasa tattalin arzikin kasa, musamman
ganin bangaren albarkatun man fetur ya fara zama koma baya.Advertisement

labarai

%d bloggers like this: