Connect with us

KIWON LAFIYA

Samar Da Tsaftataccen Ruwa Na Iya Magance Cututtuka A Nijeriya, Inji UNICEF

Published

on

Asusun yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya bayyana cear samun ruwan sha mai tsafta, da kuma tsaftace muhalli, da kuma kula da lafiyar jiki, yana iya kare yare daga kamuwa da cutar gudawa da kuma rashin lafiyayyen abinci.
An bayyana cewar rashin samun lafiyayyen ruwan sha, da kuma yin kashi a waje, da kuma al’amarin daya shafi rashin tsaftace muhalli, sai kuma yin kashi a waje, an alakanta hakan da ummul habaisun kamuwa da cutar da take nasaba da zawo, wanda kuma daga karshe yana shafar kananan yara, musamman ma wadanda basu kai shekaru biyar ba.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ake yin taron manema labarai akan al’amarin daya shafi tsaftataccen ruwan sha da kuma kula da lafiya (WASH) wanda cibiyar kula da hakkokin yara (CRIB) wadda ke karkashin ma’akatar yada labarai ta tarayya tare da hadin guiwa na asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da kuma hadin kan Tarayyar Turai EU, wanda aka yi a Awka bada dadea ba. Wani kwararre akan (WASH) shima karkashin UNICEF Ms Mainga Banda, ta bayyana cewar, idan aka yi zao sau biyar matsalar tana iya kasancewa rashin isasshen isasshen abinci mai gina jiki.
Ta bayyana cewar WASH tana da babbar gudunmawar da za ta iya badawa,amma sai dai kawai wajen alk’amarin daya shafi zawo, amma kuma a kokarin da ake yi na hana aukuwar cututtukan da aka yiwatsi dasu, amma kuma suna da illa, wadanda kuma tace kamar kisan mummuke ne suke yi. Amma kuma tace Nijeriya tana yin kokari,ta bangaren samar da ruwa, amma kuma babbar matsalar ita ce tsaftace muhalli, saboda klua milyoyin mutane a kauyuka, har yanzu basu da masai, TP taps, sai kuma abubuwan da ake amfani dasu wajen wanke hannuwa da dai sauransu.
‘’Rashin tsaida hankali akan WASH na iya samar da matsaloli da suka hada da mutuwa, saboda kuwa uwa wadda bata dadewa da haihuwa ba, tana iya sa abin da ta Haifa ya kamau da matsala, saboda kawai bata wanke hannunta ba. Amma kuma idan a an kulawa da lafiyar jiki ita matar tana iya kare shi dan nata daga kamuwa da sepsis ko kuma mutuwa da kashi 15.’’
‘’Matsalar WASH tana kao matsala akan yara masu zuwa makaranta, saboda yaro anda yake fama da cutar, ta hanyar zawon da yayi da yawa, zai kasance karshe ya samu matsala ta bai da wata laka, saboda ya rasa wasu abubuwa da suka shafi lafiyayyen abinci, zai iya kin zua makaranta, wannan kuma zai shafi yadda zai maida hankali akan abubun da ake koyamasa.’’
Ta bada bayanin cewar idan ana kulaa da lafiyar jiki, da kuma tsaftace muhalli, mata da ‘yan mata zasu iya kare martabarsu, saboda kuwa su ‘yanmata kimarsu na iya dakushewa, su kuma daina zuwa makaranta, saboda yadda zasu yi da al’ada da wata wata.
Da take kara jaddada muhimmancin rashin kula da WASH musamman akan kula da ci gaban lafiyar yara, ta ce matsalar ba karama bace, don haka tana bukatar babbar amsa yadda za a tunkari shi al’amarin.
Ta kara bayanin cewar asusunn yara na majalisar dinkin duniya zai ci gaba da kara sa himma akan al’amarin WASH da kuma sauran wasu al’amura da suka shafiu lafiyar mutum,musamman ma a wuraren da suke da sha gagwarmayar rayuwa..
Bugu da kari kuma Manajan tsare tsraen na Hukumar samar da ruwan sha da kuma tsaftace muhalli na kauyuka, wadda take karkashin kulaar ma’aikatar kulawa da abubuan more rayuwa, da kuma albarkatun ruwa, na jihar Anambra Ezekwo Bictor ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta himmatu wajen tsarin WASH, ya kuma kara da jaddada shi gamnan jihar Willie Obiano ya gyara rijiyoyin burtsatsa 116 a fadin jihar.
‘’An kammala ayyukan samar da ruwa 33, da kuma kammala gyare gyaren wasu rijiyoyin burtsatse guda 11, wadanda ada basu yin aikin komai’’.
Shi ma da yake bada tashi gudunmawar mataimakin Darekta na ata cibiya mai kulawa da cibiyar samar da hakkokin yara, a karkashinma’aikatar yada labarai da al’adu Mrb Olamide Osanyinpeju, ya jijjinawa Asusan kula da yara na majalisar dinkin duniya, da kuma Nahiyar Turai, saboda gudunmaar da suka bada, ta tabbatar da ansamu tsaftataccen ruwa, kulawa da tsaftace muhalli, da kuma kula da lafiyar jiki, sune al’umma suke bkata , musamman ma na karkara, t a hanyar tsarin WASH.
Kamar dai yadda kowa ya sani al’amarin daya shafi ruwa tsaftatacce , ba wani abin da za a yi wasa da shi bane, ga kuma maganar tsafatace muhalli, abubuwan suka shafi cigaban al’umma a Nijeriya, saboda shi al;marin da ya shafi al’umma.
Osanyinpeju ya bayyana cewar su ‘’Muradan c i gaba ko kuma sustainable Debelopments Goal (SDG) sun bayyana muhimmancin tsafatataccen ruwan sha, tsfatace al’amarin ruwan sha suna da matukar muhimmanci ga ci gaban rayuwar yara, sai kuma wani abin da shi mai sauki ne, na kula da ata karamar dabara ta kula da anke hannu saboda a kare rayukan wasu mutane.
Shi ma atashi gudunmawar wanikwararre a bangaren sadarawa na Asusun kulawa da kananan yara n amajalisar dinkin duniya Mr Geoffrey Njoku, ya gano ganawa ta hanyar tuntubar juna tana taimakawa, a kuma hada da kafa ta, domin agane muhimmancin wasu daukin da take kawowa
Njoku ya ci gaba da cewar wannan wata dama ce gas u manema labarai, saboda sun labari wadanda suka shafi al’umma, ya kamata a rika taimakawa gwamnati saboda ta kara kaimi wajen, sa hannun jari, musamman ma ala’amrin daya shafa kawo daukun dac WASH yayi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: