A samar Da ’Yan Sandan Jihohi, Inji Gwamnoni

Gwamnoni 36 na kasar nan sun amince da kirkiro da rundunar ‘yansanda mallakar jihohi domin magance karuwar rashin tsaron dake addabar kasar nan.

Shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan Alhaji Abdulaziz Yari, ne ya bayyana haka a taron kasa kan tsaro da majalisar dattijai ta shirya ranar Litini a Abuja. Amincewar gwamnonin ya biyo bayan goyon bayan da shirin ya samu ne daga mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo kwanakin baya.

Alhaji  Abdulaziz Yari, wanda shi ne gwamnan jihar Zamfara ya ce kirkiro da ‘yansanda mallakar jihohi zai magance matsalolin tsaro da tashe-tashen  hankullan da ake fama dasu a wasu bangarorin na kasar nan. Mataimakin shugaban kasar ya amince da gwamnatin tarayya da tsame hannun ta daga harkokin ‘yansanda a bar wa jihohi harkokinsu.

“Lamarin ‘yansanda mallakar jihohi abu ne ya kamata mu rugunma” in ji Osinbanjo a taron yini biyu da majalisar dattijai ta shirya akan kashe-kashen da ake danganta su da Fulani Makiyaya da sauran aiyyukan ta’addanci a fadin tarayyar kasar nan.

Farfesa Osinbanjo, ya kalubalanci masu cewa shugaba Buhari baya katabus wajen kawo karshen ta’addancin da makiyaya Fulani ke yi saboda asalinsa na Fulani, “Wannan karya ce tsagwaron ta, shugaba Buhari ba ya kare Fulani masu aikata laifi.

Osinbajo ta kara da cewa, “Na samu zuwa kauyen Dong a jihar Adamawa in da Makiyaya suka kai harin ta’addanci amma kuma kisan da aka yi wa Fulani shi ma a Adamawa abin a yi bayani a kai ne.

“Ina tabbatar da cewa, duk dan kasa na da hakkin a kare masa rayuwa da dukiyoyinsa a duk in da ya ke a fadin kasar nan, sai a kan samu akasin haka a wasu lokutta to wannan ba sakaci aka yi da gangan ba”

“Duk wani kisa da aka yi a kasar nan ya na kalubalantar mune a mastayinmu na gwamnati, shi ne ya sa bayanan da wasu ke yi na cewa, wai saboda shugaban kasa Fulani ne shi ya sa ya ke kawar da kai da kashen-kashen da makiyaya ke yi ya zama karya kuma rashin adalci ne’

“Rikicin Makiyaya da Manoma abu ne da ke tare da mu fiye da shekara 20, ni kuma ina tare da shugaba Buhari a matsayin mataimakinsa a halin yanzu fiye da shekara 3, na san maganan rikicin Makiyaya da sauran jama’ar kasa na daya daga cikin abin dake ci wa Shugaba Buhari tuwo a kwarya matuka”

“Cikin matakan da muka dauka domin kawo karshen matsalar shi ne tura ‘yan sanda ko ta kwana (Mobile) da sojojin kasa dana sama sassan jihar Binuwai, a cikin ‘yan kwanakin nan rundunar sojojin na aiki yadda ya kamata a wurare irin su kananan hukumomin Agatu da  Katsina Ala da kuma Logo”

“An kuma baza sojoji a wasu bangaren jihar Nasarawa domin maganin wuraren da ake zargin Makiyaya na amfani dasu wajen kai hari ciin jihar Binuwai, babu kokrin da ya yi yawa in dai Magana kare rayuka da dukiyoyin jama’amu ne”

“A bayyana yake dole a samu canji a kan yadda a ke tafiyar da harkokin kiwo da safararn shanu a kasar nan musamman in ana son amfana dasu ta fannin bunkasar tattalin arziki za a fi amfana da shanaye in har suna killace a wuri daya”.

“Gwamnatin tarayya ba zata dankara wa jihohi yadda zasu sarrafa filayen su ba, wannan ya zama dole ne saboda dokan kasa ta “Land Use Act” ta shekara 1978 ya mallaka wa gwamnoni ne tafiyar da harkokin tafi da filaye a kasar nan”

 

Exit mobile version