Connect with us

LABARAI

Samar Da ‘Yan Takara Na Kwarai Ne Hanyar Da Zata Baiwa APC Samun Nasarar Zabe –Tafida

Published

on

An nemi jam’iyyar APC mai mulki da ta tabbatar ta baiwa jama’a damar zaben mutanen da suke kyautata zaton zasu kawo cigaba idan an zabe su a kasa, duba da irin nasarar da canji ya kawo a wannan kasa. Alhaji Nasiru Tafida, shugaban kungiyar SABE Niger State Group ne ya yi kiran a lokacin da jam’iyyar ke shirye shirye zaben fidda gwani a ranar alhamis cin nan.

Tafida yace ganin yadda maigirma gwamna ya buga gaba ya bada damar zaben ‘yar tike ya nuna cewar siyasa ta fara tafiya da kafarta na ganin an baiwa talaka damar zabin abinda yake so. Ya kamata in haka ne kuwa a jam’iyyar ta tabbatar ba tai katsalandan ba wajen baiwa ‘yayan jam’iyyar zabin abinda suke bukata.

Tafida yace a koda yaushe idan irin wannan lokaci ‘yan siyasa kan yi anfani da ‘yan uwan mu matasa wajen bangar siyasa da tada zaune tsaye, yace lokaci ya yi da mu matasa zamu guji irin wannan muguwar dabi’ar domin ba inda zai kai rayuwar mu sai koma baya. Mun godewa Allah ganin majalisar dokokin jihar Neja na kokarin ganin tayi doka kan bangar siyasa, dan haka ina jawo hankalin majalisa da ta gaggauta ganin wannan dokar ya tabbata, don damar matasan mu yau sun samu kansu a shaye shaye da dabanci ta dalilin bangar siyasa.

Ina jawo hankalin maigirma gwamna ganin shi matashi ne da ya kara azama wajen inganta kyawawan manufofinsa akan inganta rayuwar al’umma da kawo cigaba mai anfani a jiha.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: