Abubakar Abba" />

Samfarin Cowpea Na Kwankwaso Na Samar Ma Na Da Riba – Manoma

Aikin Noma

Duk da tsananin zafin Ranar da ake fama dashi a jihar Biniwe, Manoman cowpea samfarinsa da ake kira ‘Kwankwaso,’ Manoman ba su ja da bayan ba ganin cewar yadda a tsanake suke shiga cikin lungu da sako na gonar da suka shuka cowpea wanda mallakar Jami’ar Aikin Gona (FUAM) dake a Markodi babban birnin jihar ta Biniwe.

Manoman suna yin zagaye a cikin ginar ta Cowpea, ta hanyar sanya idon masu gudanar da bincike da suka fito daga bangarori da ban-da-ban a fannin aikin noma.

Manoman na Cowpea an zabo su ne daga wurare da ban-da-ban na jihar ta Biniwe domin su fadi kalar cowpea da suke bukatar su shuka don a inga Irin na Cowpea da za’ a sarrafa shi din sayarwa.

Aikin wanda akafi sani dabarun inganta Irin Cowpea da tura shi zuwa nahiyar Afirka (ABISA), inda ake lura da Cowpea din a Gonar kasuwanci ta Jami’ar FUAM tare da hadaka da Cibiyar Aikin Gona ta kasa da kasa (IITA). Gidauniyar Bill da Melinda Gates da ABISA ana bukatar zasu fitar da gwaje-gwaje na wucin  kan sarrafa Irin Cowpea na ABISA ga wadanda suke a fannin a kasar nan.

A cewar Teryima Iorlamen, aikin zai kuma bai wa Manoman Cowpea damar jurewa barbararsa ta kara karuwa kuma duk abinda akeyi, zamu kaiwa Manoman na Cowpea don su gani ko zasu iya rungumar dabarun..

Ya cigba da cewa, wannan aikin, ya hadada kaiwar da (ABISA) zata yi Manoman na Cowpea a cikin filin don su ganewa Idanuwansu don suyi zabin da suke bukata da aka kai masu, ida zasu tabbatar cewa, ko gaskiya ce.

A cewar Iorlamen, aikin ana gudanar dashi a kasashe bakwai harda Nijeriya kuma Jami’ar ta FUAM, tana kula da tsarin na Irin Cowpea a kasar nan.

Ya ce, akwai kala-kala ns cowpea fiye da 50 a Nijeriya, inda daga ciki aka zabo 10 da sukafi dacewa aka shuka su duk a yankunan noma dake kasar nan don sga irin amfanin da zasu bayar.

A cewar Teryima Iorlamen, nau’ukan 10na Cowpea da aka shuka a gonar ta FUAM dake jihar Biniwe shine dalilin taron wanda kuma ya baiwa Manoman na Cowpea damar kwatanta daukacin sauran nau’unkan na Cowpea don su zabi wand sukafi bukata.

Ya zayyana kala-kalar da suka hada da, FUMPEA I da II, SAMPEA 11, 14, 15, 16, 17, 18, 19 da na mai kwanula 40 na samfarin (Kwankwaso).

Sun kuma yi dubi kan yadda ake nuna da wuri kafin yin subi akan launin Irin, inda kuma hakan ya nuna ba su da damu da yin dubi kan girman Irin ba, in har aun zabi Irin da sukafi bukata.

A nasa jawabin sa a wurin taron, wakilin Manajan shirin IITA dake a jihar Kano kuma wani babban mai gudanar da bincike a fannin Rueben Solomon ya sanar da cewa, Nijeriya tana daya daga cikin kasashen dake kan gaba wajen noman Cowpea a duniya.

Binuwe kusan ta na gaba da sauran jihohi wajen noman Cowpea a Nijeriya domin daga abinda mu ka iya gani, Binuwe ta yi wa sauran jihohin kasar nan zarrafa wajen noman Cowpea domin a hankali-a hankali, jihar sai kara tsayawa take da kafafunta wajen noman Cowpea.

Solomon ya kuma jadda da cewa, manufar aikin shine, “Muna son mu janyo Manoman na Cowpea ne a jiki tun daga kasa har zuwa sama kafin mu saki Irin na Cowpea.

Masu binciken suna son Manoman na Cowpea su zabi Irin na Cowpea da su ka fi so kuma wanda su ka zaba, dashi ne za’ayi amfani.

“Za mu cigaba da bayar da shawarwari idan mun dawo wani yin gwajin, inda ya yi nuni da cewa, kasar jihar Biniwe ta na da kyau wajen noman Cowpea.’’

Tunda farko, babban Manomin cowpea a jihar ta Biniwe Crucial Abua a wajen gudanar da aikin ya shaida wa jaridar Banguard cewa, ya mallaki kadada 10 da ake noman Cowpea a yankin Gboko dake cikin jihar ta Biniwe, wadda ya kara da cewa, za’a yi  girbi nan da yan kwanuka.

Abua, wanda kuma har ila yau shi ne mai bai wa Ministan Ayyuka na Musamman shawara George Akume shawara ne, ya kara da cewa, an shuka kala biyu na Cowpea samfarin FUMPEA II da kum na SAMPEA II a gonarsa, inda ya kara da cewa, na FUMPEA II ya kamu da chututtuka da dama, inda hakan ya nuna cewa akwai ban-banci waje yakar kwari.

Su ma’aikatan, tuni sun fara girbi a FUMPEA II kuna zan iya sheda maka cewa, harbin bai kai kasa da kashi biyu cikin dari ba wato ma’ana, harbuwar kusa,take da sufuli.

Sai dai, harbuwar ta SAMPEA II, ta na da yawawas, inda hakan ya sanya na gabatar  (IMI-Force), wanda, ya na karfi sosai.

Abua, wanda har ila yau mai bai wa masu binciken ne shawara ta mussaman ne ya yabawa masu binciken kan jajircewar su don  inganta Irin na Cowpea.

A wata sabuwa kuwa, Kwantrolan hukumar kwastam shiyar Zone B, jihar Kaduna, Mustapha Sarkin Kebbi, ya bayyana cewa hukumar ta gano hanyoyi 2000 da ake amfani dasu wajen yin fasa kaurin shinkafa da wasu haramtattun kayayyaki ta Arewacin kasar nan.

A cewar Kwantrolan hukumar kwastam shiyar Zone B, jihar Kaduna, Mustapha Sarkin Kebbi, hukumar kwastam ba tada karfin ma’aikatan da za su tsare dukkan wadannan barayin hanyoyin amma suna iyakan kokarin ta wajen tabbatar da cewa shinkafar wajen ba su shigowa cikin kasar nan ba.

Kwanturolan wanda ya shedawa manema hakan a kaduna ya kuma zayyana wasu nasarori da yankinsa ta samau wajen dakile masu fasa kwabri.

Ya bayyana cewa an kuma kama kayyaki da dama da su ka hada da, motoci, shinkafa, man gyada, taliya da sauransu a jihohin Katsina, Sokoto, Kebbi da Kwara.

Kayan su ne kamar haka, motoci 25 da Buhunhunan shinkafa 703 da galan din man gyada 530. Sauran kayan su ne, kwalayen taliya 245 da dilolin kayan gwanjo 9 da galan din Kalanzir 40 da tankar man fetur da galan man fetur 288.

A wata sabuwa kuwa, Ministan sadarwa, Isa Pantami, ya shawarci hukumar kwastam ta da ta dakatar da dokar hana kai man fetur garuruwan da ke kusa iyakokin kasar nan, inda ya yi nuni fa cewa, hakan ya zama babban kalubalen da ma’aikatarsa ke fuskanta.

Jaridar Premium Times ce ta ruwaito mai magana da yawun minstan, Uwa Suleiman ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya, inda sanarwar ta kara da cewa, hakan zai bayar da dama kamfanonin sadarwa su tayar da injinan wutar su ta lantarki don samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar nan.

Exit mobile version