Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Samfuran Kalaman Soyayya

by
4 years ago
in SOYAYYA
4 min read
Samfuran Kalaman Soyayya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Kamar dai yadda wannan shafi ya saba kawo muku abubuwan da suka shafi Soyayya, a yau ma wannan shafi yana dauke da kalaman da suka shafi Masoya sai ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi na SOYAYYA DA SHAKUWA.

 

Ga kuma kalaman:

Labarai Masu Nasaba

Soyayyar Zamani, Nagarta Ko Kyalkyali?

Duk Namijin Da Bai Mallaki Zuciyar Mace Ba Rashin Cancantarsa Ne Sila

Yake annurin zuciyarta ki nutsu ki saurari zuciya ki ji abin da za ta fada a kanki yake hubbina.

  • Ina sauraranta yayin kuma da hankalina da zuciyata suka ta’allaka a kanka, ya kai sanyin idaniyata.
  • A duk lokacin da taurari suka haska sararin samaniya ni kuma a wannan lokacin hasken kyakkyawar fuskarki ke haskaka idanuwana, yake annashuwar zuciyata, yake burin zuciyata raina fansa ne a kanki yake hasken ruhina a bar sona a bar begena a kodayaushe.
  • Na yi farin ciki yayin da na san kai ne zabin zuciyata kuma me sanyaya mata kowane lokaci.
  • ke ce masoyiyata ke ce nake ji a zuciyata ke ce duniyata saboda ke ce rayuwata masoyiyata ki matso kusa da ni a kowane lokaci nakan yi kewarki a kowane dare nakan taba tunaninki.
  • Zan so mu rayu kuma mu mutu tare a cikin taska wadda ta kasance daga masoya kuma hadaddu.
  • Ya ke masoyiyata hasken ruhina akwai suddabaru a tattare da ke akwai kamshin farin ciki a jikinki wanda ni kadai nakan ji hakan da bugun zuciyata my lobe.
  • Kar ka yi tunani ko tantama a kan soyayyata ya kai masoyina ka kalli hannuna na dama yayin kuma da nake so ka rufe idanunka kyauta ce zan ba ka daga cikin zuciyata, Na kira ka my lollipop na kira ka my sweet angel mataye da dama na hange daga nesa amma na san ba za su hango abin da idaniyata suka gani ba.
  • Allah na gode ma da ka ba ni aminiyar zuciyata wacce a kodayaushe zuciyata take bugawa a kanta masoyiya, soyayyarki ta riga ta yi min diban-karan-mahaukaciya.
  • Nakan yi tunani a cikin kaya taccen lambun soyayya wanda ya cika da kayan marmari zo ka rike hannuna masoyi rabuwa da kai kamar karewar kayan marmari ne a cikin kayataccen lambu.
  • Na taho na miko hannuna izuwa gare ki yake kaddaran zuciyata a shirye nake da in amsa babbar kyauta daga zuciyar da ta fi kowane zuciya kyawu wacce kyawun ta tafita zinare kyau da kyalkyali.
  • Na gode da nuna soyayya tabbas ka cancanta ka karbi babban kambu wanda ya gagari maza da dama ya kai abin alfaharina kuma mafarkina.
  • Abar so na na taho na miko hannuna gare ki ki miko min hannunki mai laushi tamkar tumfafiya in kai ki lambun masoya ki bude kyakkyawar bakinki mai cike da hasken annashuwa in tsinki tuffa in ciyar da mallakar zuciyata in shayar da ke giyar soyayya ta ki bugu a cikin soyayya ta yake a bar kaunata.
  • Godiya nake ya kai gwarzona kuma jarumi abin alfahari nakan ji haske da nishadi idan ina tare da kai yaka taho masoyi mu zauna na yi ma hirar masoya kwalelen makiya.
  • Wow you are my lobe i feel you in my heart because you my heart and U my soul eber day i miss you baby eber night i miss you touch ke ce al jannata dausayina ke ce soyayyata ke ce mallakata burina ke ce annashuwar zuciyata na baki kaina da kaina yake my heart.
  • I don’t know what is life without you, I am mighty glad that God gabe you to me and my dream comes true don’t leabe me my lollipop. Matsayika ya tabbata a cikin fadar zuciyata mai tattare da shimfidu na alfarma mai dauke da jajayen furanni wanda suka haskaka domin soyayyar ka my only.
  • Na ji kira na amsa ya ke hasken ruhina makiya sun buga sun kasa na riga na musu fintinkau a kan soyayyarki tuni na dade da mallaka miki fadar zuciyata ke kadai ce kike mulkin mallaka a cikin ilahirin birnin zuciyata.
  • Tabbas na durkusa na karbi wannan kyauta daga kyakykyawan masoyi mai kyawun aniya manufata ita ce na mallake ka domin idan ban mallake ka ba to tabbas zuciyata tana cikin sarka a daure yayin da ruhi zai kasance ba a gangar jiki ba.
  • Hakika na zama sarkin zuciyarki kin zama sarauniyar zuciyata my heartbeat na shigo zuciyarki mai cike da tsananin kyawu wanda babu irinsa a duniya wanda a cikinta na samu annashuwar tawa zuciyar. Wayyo masoyiyata daina wannan maganar a kodayaushe ke ce burin zuciyata ki sani ni wata ke ce zara ta a kowane lokaci ba ma rabuwa na juna hanta kin zamo jinin hantar wanda a kodayaushe daya ba zai iya rabuwa da daya ba zan so ki zama madara in zama suga mu hadu a kwaryar soyayya.
  • Kar ka yi tunanin zan daina sonka amma ka yi tunanin yadda zamanmu zai kasance cikin yadda da a mana my lobe.
  • A kodayaushe tunanina da naki daya ne wanda ni na fassara na ki ke ma kika fassara nawa fassarar kuma kala daya ce shi ne ni da ke mutu ka raba takalmin kaza hakika ni da ke za mu yi zama na amana har sai mun bar tarihin soyayyar da babu wasu masoya da suka bar kalarsa ya ke bugun zuciyata a bar kaunata shirunki na minti daya a gare ni ba karamin asara ba ne a zuciyata maganarki kadai yakan annashuwar zuciyata ne.
  • Ina tare da kai ya kai madarar idaniya mai sa zuciya farin ciki ka kasance mutum mai farin jini cikin kokon raina ba zan iya tuna sau nawa nake mararinka ba ka kula da ni zan ba ka soyayya zan ba ka madara wadda tafi zuma masoyina.
  • Ku gafara ku ba ni wuri in yabi my kueen heart dina kyunki tum hi ho ab tum hi ho zindagi ab tum hi ho only for you in my heart, hakika na san cewa zara ba ta iya nisa da wata hakika na yi dace da samun sarauniyar kyawawan matan duniya kuma farin cikin zuciyata burin ruhina.
  • Na fika san na yabeka my sweet lobe domin ina so duniya ta shaida ba ni da wani wanda ya fika kuma zuciyata kai take marari cikin dare ko rana safiya ko yamma zaune a kwance nakan yi murmushi idan na tuna cewa tomorrow will belongs to me my beautiful handsome my oga,Idan nayi duba izuwa masoya nakan ga kamar nasu wasane, amma na kan yi alfahari da soyayyarmu Kai ne ka sa na zamo ta daban a rayuwata, godiya Ga hadadde kuma hadadde a cikin masoya.

Ku tara mako mai zuwa domin jin da me zan zo muku da shi

 

Tambayarmu Ta Wannan Makon Na Cewa:

Me yake saurin kawo mutuwar Aure a wannan zamanin?

Shin masoyan ne ba sa auren junansu ko kuwa soyayyar ce take kare wa da zarar an yi aure? Shin ya abin yake ne, yi bayani a takaice?

Sai na ji daga gare ku_

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Ina Rokon Ku Zabi Dantakararmu A Zaben Cike Gurbi Na Bauchi – Buhari

Next Post

Siffofin Da Mata Ya Kamata Su Lura Wajen Zabar Mijin Aure

Labarai Masu Nasaba

Soyayyar Zamani

Soyayyar Zamani, Nagarta Ko Kyalkyali?

by
1 year ago
0

...

Soyayyar Zamani

Duk Namijin Da Bai Mallaki Zuciyar Mace Ba Rashin Cancantarsa Ne Sila

by
2 years ago
0

...

Me Ya Sa Mu Ke Yin Soyayya?

“Akwai Wasu Abubuwan Da Masoya Ba Su So A Lokacin Zance”

by
2 years ago
0

...

Alamomi Dake Nuna Cewa Soyayya Ta Kare Tsakanin Ki Da Namiji

by
2 years ago
0

...

Next Post
Siffofin  Da  Mata Ya Kamata Su Lura Wajen Zabar Mijin Aure

Siffofin Da Mata Ya Kamata Su Lura Wajen Zabar Mijin Aure

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: