Samir Nasri Ya Koma Westham

Kungiyar kwallon kafa ta Westham ta kasar Ingila ta kammala daukar dan wasa Samir Nasri bayan dan wasan ya sha fe wata da watanni a kungiyar yana daukar horo kuma zai fara bugawa kungiyar wasa da zarar lokacin da aka dakatar dashi ya cika.
A shekarar data gabata ne dai aka dakatar da dan wasa Nasri na tsawon shekara daya sakamakon kamashi da akayi da laifin kin zuwa domin a gwada jininsa a gani ko yana shan kwayoyi masu kara kuzari.
Nasri ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Marseille ta kasar Faransa inda anan yafara buga kwallonsa daga baya kuma ya koma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a lokacin tsohon kociyan kungiyar Arsene Wenger.
Nasri ya bar kungiyar Arsenal inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester City kafin kuma daga baya yaje kungiyar kwallon kafa ta Sebilla ta kasar Sipaniya a matsyain aro inda daga nan kuma kungiyar kwallon kafa ta Antalyspor ta kasar Turkiyya ta siye shi.
“Na ji dadin samun dan wasa mai kwarewa kamar ta Nasri saboda babban dan wasa ne wanda kuma zai taimakawa kungiyar nan kuma nasanshi sosai tun muna kungiyar Manchester City” in ji Manuel Pelligrini, kociyan Westham wanda tsohon kociyan Manchester City ne
Ya ci gaba da cewa “Nasri zai taimaka mana sosai wajen kara karfin kungiyar mu a wannan lokacin da aka raba gasar firimiya kuma yana da kwarewa yadda yakamata wadda magoya bayan mu za suga amfanin daukansa nan gaba kadan.
Samir Nasri dai ya lashe gasar firimiya guda biyu a Manchester City inda ya lashe a kakar wasa ta 2011 zuwa ta 2012 sannan ya sake lashewa a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014 duka a lokacin mai koyarwa Pellegrini.

Exit mobile version