Daga Mustapha Ibrahim, Kano
Hukumar kula da yanayi ta Nigeriya watau Nigeria Hydrological Serbices Agency.NIHSA ta bayana cewa yanzu haka an samu ambaliyar ruwa a jahohi 27 nakasar nana a wannan shekara ta 2017.Wannan bayanin yafito ne daga bakin babban Jami’i mai kula da Arewa maso-Yamma Yunusa Yahaya Hashimu Kano, a yayin wani taro da hukumar ta shirya a ranar Litinin din nan data gabata. Haka kuma yace yanzu haka an rasa mutane sama da 60 wadanda suka rasu a wadannan jihohi 27 Inda ya ce a Jihar Neja mutum sama da 40 suka rasusai kuma jihar Gwambe mai sama da mutum 20 da Milliyoyin Nairori, dan haka yayi kira ga Jama’a a kan su kula da muhalli kuma yadda ya kamata.
Shi ma a jawabinsa Darakta mai kula da bin didigin aiki a ma’aikatar kula da muhali ta Kano Dakta Garba Saleh Ahamad wanda kuma shi ne ya walkicikwamishinan muhali na Kano Honarabil Ali Bukar Makoda, ya bayyana cewa manyan dalililai biyu ne ke kawu Ambaliyar Ruwa.Na farko daiyanayi da kuma gini-gine a hanyoyin ruwa.
Haka kuma Dakta Garba ya ce, a Gwamnatin Kano kashe kudi kimanin Naira Billiyan Biyu a kokarinta na daukar mataikai a kan matsalar Ambaliyar Ruwa. Dan haka ya shawarci Jama’a da su kula da tsaftar muhali da kuma nemanizinin Hukumomi a duk lokacin da zaayi wani gini.