A wata tattaunawa ta musamman da LEADERSHIP A YAU ta yi a kwanakin baya tare da shugaban hadakar ‘yan kasuwa na karamar hukumar Damaturu cikin Jihar Yobe Alhaji Garba Bazam, shugaban ya bayyana irin halin da mambobin kungiyar suka shiga na sukurkucewar harkokin kasuwancinsu sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro da yankinsu ya yi fama da shi da yadda gwamnatin jihar ta yi ta kokarin dafa musu don fita daga wannan halin kunci. Ga dai yadda hirar ta kasance, a sha karatu lafiya:
Yaya tarihin wannan kungiya taku yake da kuma adadin mambobin ku?
To ita wannan hadakar kungiya tamu ta hadakar ‘yan kasuwar garin Damaturu mun kafa ta ne fiye da shekaru goma da suka gabata.
Kuma a yanzu haka muna da akalla mambobi fiye da dubu goma wadanda suke cikin kudinmu.
Mambobin kungiyar nan taku sun hadu da ibtila’i iri-iri a ‘yan shekarun nan a dalilin tabarbarewar harkokin tsaro, ko yaya abin yake ne?
Lalle kam mambobin wannan kungiya tamu sun hadu da ibtila’i
daga Allah (SWT) lokuta daban-daba kama ga konewar dukiya sanadiyyar tashin gobara ya zuwa konewar dukiya sakamakon
hare-haren ‘yan bindiga da ya kai ga hasarar rayuka da dukiya na milyoyin nairori. Da kuma karayar tattalin arziki da wannan lamari ya haifar wa aksarin ‘yan kasuwar.
Har ila yau, matsalar tabarbarewar tsaro ta haifar da mummunan koma baya ga harkokin kasuwancin wannan yanki namu ta yadda za ka tarar a ‘yan shekarun baya mutum daya kan sauke kaya fiye da tirela uku a duk mako amma sai da ta kai da lamurra suka yi kamarin da, da kyar za ka sayar da buhu goma kacal a mako. To ai ka ga mun ga jarrabawa iri-iri.
Yanzu fa yaya abin yake idan aka kwatanta shi da shekaru uku da suka shude?
Ko akwai wani tallafi da gwamnatin Jihar Yobe ta ba ku sakamakon jarrabawan da suka shafi wasu mambobinku?
Alal hakika gwamnatin Jihar Yobe a karkashin mai girma gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ta yi matukar tallafa wa mambobinmu da lamarin ya shafa. Domin kuwa, akwai lokacin da aka yi gobara a cikin babbar tashar motar Damaturu inda mambobinmu suka yi hasarar shagunansu da dukiyoyinsu amma da gwamnan ya zo ya gani sai ya bada umarnin a kiyasta hasarar da kowane dan kasuwa ya yi, da muka yi kiyasi muka kai masa cikin kwanaki hudu kacal ya amince da a biya mu kashi dari bisa dari na dukkanin kiyasin da aka kai masa yadda ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA a takaice, da ta ba mu Naira miliyan goma sha takwas don raba wa ‘yan kasuwar da hasarar ta shafa.
Haka nan, a wancan lokacin ma da mambobinmu suka hadu da ibtila’in hare-haren 1 ga watan Disamban 2014, inda shaguna kusan 78 suka salwanta bayan da gwamna ya zo ya gani da idonsa tare da jajantawa da kuma wasu wurare akalla biyar da suka hadu da gobarar shugaban bai yi kasa a gwiwa ba ya amince da a ba mu tallafin kudade sama da Naira miliyan sittin don tallafa wa wadanda suka sami kansu cikin ibtila’in. Don haka babu abin da za mu ce wa gwamnatin Jihar Yobe da Gwamna Ibrahim Gaidam sai dai fatan alheri domin kuwa alama ce mai nuni da cewar lallai gwamnan na tare da jama’arsa kana yana kuma tausaya musu.
Ko kuna da wani koke ko korafi ga gwamnatin jiha da kuma ta tarayya dangane da wasu bukatunku?
Babu shakka, shi da ai ba ya gajiya da kuka ga mahaifinsa duk irin taimakon da ya ba shi. Hakika kungiyarmu tana sake neman taimako daga gwamnatin Jihar Yobe dangane da bada jari ga ‘yan kasuwar da suka karye sanadiyyar tabarbarewar tsaron da yankin ya yi fama da ita, kasancewar aksarin ‘yan kasuwa rashin ishasshen jari na ci musu tuwo a kwarya, kuma jarin ko da rance ne da ba shi da ruwa mai yawa muna bukatarsa.
Haka ma ta bangaren Gwamnatin Tarayya muna rokon ta da ta kawo mana dauki. Kodayake da ma muna tsammanin hakan daga sabon shugabanmu mai adalci Shugaba Muhammadu Buhari kasancewar a kullum tun daga hawansa karagar mulki yake bayanin cewar zai mayar da hankalinsa ga wannan yanki namu kuma ko yanzu mun gani a kasa tun da tuni ya maido da karfin tsaron kasa ga wannan yankinmu don kokarin dawo mana da yanayin tsaro mai inganci.
Allah Ya taimaka.
Madallah na gode, Allah Ya albarakaci wannan jarida tamu.