An Samu Gaggarumin Taimako A Wajen Gangamin Katange Makarbatar Garin Dutsen-wai

A cikin makon da ya gabata ne jama’ a garin Dutsen-wai dake karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna suka yi ruwan bulon suminti a lokacin da wata kungiya mai kokarin kawo ci gaban garin ta yi kira zuwa gyara wasu makabartu guda biyu dake garin. Wakilinmu ya gane wa idonsa yadda bulon suminti ya yi zubo wa kamar daga sama,da farko dai shugaban kungiyar ci gaban garin Dutsenwai Alhaji Magaji Mai Kwando shi ya fara zantawa da wakilin namu ya kuma fede masa biri har wutsiya a kan yadda aka samu wannan gaggarumin taimakon daga mutanen garin

Alhaji Magaji ya fara ne da godiya ga Allah da ya ga wannan rana da jama’ar gari suka amsa kiran da kungiyar su ta yi wacce yake jagoranta don kawowa garin ci gaban rayuwa ta bangarori da dama.

Ya ce, wannan bulon na siminti da yashi da dutse da ke fitowa kamar daga sama to kiran da mukayi da azo a taimaki juna  gashi jama’an gari manya da yara masu kudi da talakawa duk sun amsa kiran da muka yi musu don zuwa gyaran kushewarmu wato makabartar guda biyu da muke dasu shekaru masu yawan gaske.

Ya ce, wannankkugiyar ce ta zauna tayi tunani kamar yadda ta saba a kullum idan wata matsala ta bijiro, to a wannan lokacin ma sun lura da ana samun koke a kan cewa, dabbobi na ratsa wa cikin makabartun wanda hakan kuma nasa suna rusa kaburbura kuma hakan bai dace a ba.

Alhaji Magaji ya ce, hakan yasa suka fitar da shawara tare da tumtubar dattawa a kan suna kira ga duk jama’ar garin Dutsenwai da kowa ya bayar da kwaran bulon siminti daya rak don katange makakabartun da dabbobi ke shiga ya ce, wannan sanarwar ce ta janyo jama’ar wannan gari bisa amanar dake tsakaninmu suka je gidajen da ake sayar da bulon su yi odar bulon daidai kafinsu shi.

Alhaji Suleman Aliyu shi ne Limamin masallacin Juma’ar garin, ya ce, wannan babban aiki duk da yana da shekaru masu yawa ya yake yiwa wakilinmu tambihi a kan wannan kokari da kungiyar take yi na kawo hadin kan jama’ar wannan gari, ya kuma kara da cewa, gaskiya babu abin cewa sai godoya tare da sanya masu albarka da basu goyan baya.

Alhaji Idris Husain shi ne babban basarake wannan gari kuma shugaban kwamitin gudanar na wannan aikin na gyaran makabartun wannda da shi ake wannan aiki har ya zanta da wakilinmu ya ce, abin ban sha’awa yau ga dan Izala da dan Darika da dan Shi’a sun hadu ana aikin taimakon juna yadce, wannan abin farin ciki ne, ya kara da cewa garin Dutsenwai na da makabartu guda biyu kuma wannan kungiyar ta shelanta neman a katangesu yanzu haka aiki ya yi nisa sai karashe don haka ya mika godiya ga iyayen kungiyar da duk jama’ar da suka bada taimako ya yi fatan Allah ya biya masu da gidan Aljanna.

Ya zuwa hada wannan labari jama’ane ke yin dafifi wajan wannan aiki, ciki harda kungiyoyi kamar kungiyar magina da kungiyar yan baro da kungiyar masu fasa dutse kuma abin sai wanda ya gani.

Bangaren Ilimi ma tuni gungiyar ci gaban na Dutsenwai ta zakulo malaman wucin gadi don taimawa makarantu kafin gwmnati ta gama tantance wandda take so don turosu makarantu.

 

Exit mobile version