Daga Abubakar Abba
Gungun ‘yan fashi da makami masu tare manyan hanyoyi da suke yunkurin yin amfani da damar bikin kirismeti sun fada a cikin komar ‘yan sanda na jihar Enugu.
’Yan fashin hudu, Kenneth Eze da Ojobo Ude da Emeka Eze da kuma Sunday Ugwu an cafke su ne lokacin da suke kokarin yiwa wasu fasinjoji fashi da suke cikin wata motar Bas a wuraren babban titin Ninth Mile/Nsukka.
An ruwaito cewar, lamarin ya auku ne a ranar 24 ga watan Disamba a lokacin da gungun ‘yan fashi shda da suke sanye da kayan ‘yan sanda suka datse hanyar .
‘yan fashin sun tilastawa aben hawa canza hanya wanda suke kan hanyar su ta zuawa jihar Legas, inda suka fantsama cikin daji.
‘Yan fashin sun karbewa fasinjojin kayan su, inda daga baya jami’an ‘yan sanda naofishin gundumar Ninth Mile suka yi kundubalar auka ‘ yan fashin.
An ruwaito cewar anyi musayar wuta tsakanin ‘yan sandan da ‘yan fashin, inda aka samu nasarar cafke mutum hudu daga cikin su biyu kuma suka arce..
Kakain rundunar ;yan sandan jihar Ebere Amaraizu, ya tabbatarda aukuwar lamarin, inda yace ‘yan fashin sun samu mummunar rauni a yin artabun da ;yan sanda.
Ebere yace, ‘yan fashin sun karkatar da abeben hawa da suka fito daga jihar legas zuwa Otukpo a cikin jihar in Benue , inda suka yiwa matafiyar fashi ‘yan sanda kuma suka auka masu.
Ya kara da cewa, gungun ‘yan fashin an kama su ne lokacin artabun da ‘;yan sanda, inda aka cafke mutum hudu wanda kuma suka gudu sun arce da mugayen raunuka kuma jami’an ‘yan sandan sun baza komar su don cafko wadanda suka arce..
A karshe ya yi kira ga al’ummar jihar dasu taimakawa da rundunar da sahihan bayanai akan ‘ yan fashin da suka arce.