Daga Sagir Abubakar
Shugaban majalissar dokoki na Jihar Katsina, Alhaji Abubakar Yahaya Kusada, ya bayyana cewa an samu ribar demokuradiyya a jihar a cikin shekaru talatin da suka gabata kuma hakan zai cigaba da kasancewa abin alfahari ga ‘yan jihar baki daya.
Shugaban majalisar ya wna musamman na bikin cika shekara talatin da samuwar Jihar Katsina a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatarensa na yada labarai, Nasiru Ahmed Zango.
Alhaji Abubakar Kusada ya ta’allaka cigaban da aka samu bisa aiki mai kyau da ke akwai tsakanin bangaren zartarwa da na ‘yan majalisa tun farkon samuwar jihar zuwa yau.
Ya jaddada cewa, gwamnatin APC mai ci yanzu za ta ci gaba da gudanar da shugabanci kamar yadda tsarin mulki ya tanada domin tabbatar da an tallafa wa talaka.
Ya yi nuni da cewa, shirin gwamnatin Masari na farfado da abubuwa kamar yadda suke zai ci gaba da samun goyon bayan majalisa domin samun cigaban da ake bukata a fadin jihar. A daga karshe, ya yi godiya ga Allah bisa samun nasarorin da jihar ta samu.