El-Mansur Abubakar" />

Sana’ar Abinci Ta Yi Min Komai A Rayuwa –Rahina Diga

Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Malama Rahina Ibrahim yar asalin garin Diga ce dake Filiya a yankin karamar hukumar Shongom ta jihar Gombe ta bayyana cewa Sana’ar sayar da abinci tayi mata rana a rayuwa domin ta samu rufin asiri.

Rahina Ibrahim, a lokacin da take zantawa da Leadership A Yau Lahadi, tace ta fara sana’ar sayar da abinci da soya masa ne yau shekara 3 da suka gabata kuma ta fara ne da jarin naira dubu uku amma zuwa yanzu tana juya jari yafi na naira dubu hamsin.

Ta ce a kowacce rana tana yin naira dubu goma zuwa dubu goma sha biyu kuma a shagon nata tana da yara masu yi mata aiki guda biyar da a kullum idan an gama kasuwa take sallamar su su ma suke cin gajiyar wannan sana’a.

Rahina Ibrahim, ta kara da cewa tana sayar da abincin ne da ya shafi Tuwa da shinkafa da kuma farfesun kayan ciki dana kananan dabba wanda daidai gwargwado ana saya kuma tana gane kasuwar.

A cewarta duk wanda ya rungumi sana’a kowacce irin ce ba zai rasa yadda zai yi a rayuwa ba sai dai idan ba mai son ci gaban rayuwar kansa bane ya kashe zuciya ya dinga zaman banza.

Ta ce yanzu haka a shangon ta dake kan hanyar zuwa gidan Abubakar Habu Hashidu tsohon gwamnan Gombe na farar hula na farko tana da Yaran shago biyar amma idan ta samu tallafi za ta iya daukar Yara kamar guda ashirin wadanda za su dinga aiki a karkashin ta wanda daukar su aiki rage zaman banza ne a tsakanin al’umma.

Rahina Diga, tace tana kiran gwamnati da ta taimaka mata da Karin jari domin ta yiwa siyasa wahala amma an bar ta a baya wanda idan aka taimaketa mutane da yawa za su ci arzikin wannan sana’a.

Ta yi amfani da wannan damar ta yi kira ga mata yan uwanta masu zaman banza na kashe zani da cewa yanzu lokaci ya yi da za su tashi su taimaki kansu domin dogaro da namiji yanzu ya wuce kuma duk wacce ba ta sana’a ko a wajen mijin ta ne ba za ta yi daraja ba saboda su ma Mazajen a wani lokaci suna son macen da za ta rage musu wahala ta wani gefe.

Malama Rahina Ibrahim tace irin rufin asirin da ta samu a wanann sana’a ta sayar da abinci ba zai misaltu ba na baya-bayan nan shi ne ta mallaki muhalli ta fita daga haya wanda wannan kadai ba karamar nasara ba ce ace yau mutum ya mallaki gida ba haya zai biya ba.

Daga nan sai ta yi amfani da wannan damar ta sake yin kira ga mata da matasa masu macecciyar zuciya da suyi koyi da ita wajen neman na kansu domin ita a kauyen Filiya take ta shigo gari dan neman na kanta kuma da yake sana’a take yi ba zaman banza ba Allah ya taimake ta asirin ta ya ruhu.

 

Exit mobile version